An zabi shugaban rukunin kamfanin jaridun Media Trust, Alhaji Kabiru Yusuf, a matsayin shugaban kungiyar masu gidajen jarida a Nijeriya, wato ‘Newspapers Proprietors of Nigeria’, (NPAN).
Zaben ya gudana ne a sakatariyar kungiyar da ke Maryland a Jihar Legas jiya Talata. Kungiyar ta NPAN ta hada dukkanin masu mallakin jaridu a fadin kasar ne.
Kabiru Yusuf, wanda ke jagorantar rukunin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da ke fita kullum da mako-mako, wadanda su ka hada da Lahadi, Tambari, YouthBilla, Kilimanjoro, Aminiya (ta harshen Hausa), Kano Chronicle gami da sauransu.