An Zabi Shugabannin Kungiyar Masu Harhada Magunguna Ta Jihar Kano

Masu Harhada Magunguna

An zabi shugabannin kungiyar harhada magunguna na jihar Kano Pharmaceutical Society of Nig. Pharm. Sani Ali Yusuf, shi ne aka aba amatsayin sabon shugaban kungiyar  Pharm. Ibrahim Jinjiri mataimakin shugaba Pharm. Gidado Yusuf sakatare, Pharm. Mustapha Umar mataimakin sakatare Pharm. Suleiman Danladi Fin. Sect, Pharm. Sani Abdullahi ma’ajin kungiya Pharm. Nasiru Rikadawa Odita, Pharm, Clement Hamidu P R O, Pharm. Bala Maikudi shi ne tsohon shugaban kungiyar na jihar Kano.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kamala zaben, sabon shugaban ya nuna godiyar shi ga Allah da ya nufa ya zama sabon shugaban kungiyar da kuma daukacin yankungiyar maza da mata .Pharm. Sani Ali Yusuf ya ce harkar magani a jihar Kano da kasa baki daya ya na da matukar hatsarin gaske sannan age guda kuma yana da muhimmanci ga rayuwar dan’adam, amma abin bakin ciki an wayi gari magunguna na jabu sun cika kasuwannin jihar dama wasu daga cikin kasuwannin kasar nan.

Saboda wadan nan matsaloli da ake fuskanta ya sa kungiyar za ta yi bakin kokarinta wajen hada kai da sauran kungiyoyin da ke hana shan miyagun kwayoyi da kuma saida su a jihaR Kano kamar hukumomin NDLEA da kuma NAFDAC da tare da ma’aikatar lafiyar ta jihar Kano musamman wadanda suke da hakkin akan hanawa.

Kungiyar har ila yau za ta yi amfani da jami’an tsaro domin ganin ana amfani dad a magunguna masu kyau. Ya kuma jinjinawa gwamnan jihar Kano akan yadda take bakin kokarin ta wajen dakile shan miyagun kwayoyi ga al’ummar jihar ga maza da mata abin bakin ciki inji shigaban kumgiyar har da matan aure. Kungiyar da hadin gwiwar da gwamnatin ta samar zuwa yanzu sun rufe shaguna kimanin biyar da su shaidar sayar da magani da kuma wadanda ba su da takardar izinin sayar da magani.

Wannan aikin na su na rufe shaguna sayar da magunguna ba bu ka’ida zai cigaba da yardar Allah. Ya kuma ce kungiyar su za ta hada kai da yanjaridu domin wayar da kan al’ummar jihar wajen illar shan miyagun kwayoyi, idan aikin ba bu ‘yan jaridu ba za’a san aikin da kungiyar take yi ba. Sai ya yi amfani da wannan dama da kira ga ‘yan kungiyar da su cigaba da baiwa kungiyar hadin kai da goyon baya kamar yadda suka sa ba, sannan kuma su tabbatar suna halartar tarukan kungiyar aduk lokacin da bukatar hakan ta sa so inji Pharm. Sani Ali Yusuf.

 

 

 

 

 

Exit mobile version