Abubakar Abba" />

An Zargi Daliban NDA Kaduna Kan Muzgunawa Matafiya

Wasu yan Nijeriya da kafafen sadarwar zamani sun bayyana bakin cikinsu dangane da damuwar yadda daliban kwalejin horas da hafsoshin Sojin Nijeriya, NDA, suke tare manyan hanyoyi tare da muzgunawa matafiya a Nijeriya.

Kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito wani bidiyon dake yawo a kafafen sadarwa da jaridar The Herald ta dora ya nuna yadda daliban su biyar sanye da kayan Sojoji suka tare hanya, wanda hakan ya janyo cunkoson ababen hawa a wani babban titi.

Wannan lamari ya zama tamkar al’ada ne ga daliban, inda suke kiransa da Plumming 101, kuma suna yinsa ne a duk lokacin hutun Kirismeti ko sabuwar shekara.

Harila yau, a cikin faifan bidiyo an hangi daliban suna rawa a kan titi, suna fareti, sauran kuma suna zagin matafiya dake neman a basu hanya su wuce.

An jiyo daya daga cikin daliban yana cewa, babu abin da zasu iya, Ubansu! Babu da zasu iya, dole ne su jira mu, ina take ne, ina take ne? haka nake so, zo mu tafi, wani shegen ne yake danna hon?

Har ila yau, a faifan bidiyo na biyu kuma an hangi daliban sun tare babban shataletalen Lebentis na Kaduna, suka hada cunkoson ababen hawa.

An tuntubi mai magana da yawun kwalejin NDA, Manjo Abubakar Abdullahi game da bidiyon, sai yace, don Allah a bani lokaci, zan mayar da martani.

Yadda mahara suka far wa garin Tawara suka kashe mutane 15

Exit mobile version