Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

An Zargin Dan Sanda Da Harbin Dan Siyasa A Legas

by
4 years ago
in Tauraruwa Mai Wutsiya
4 min read
Yadda Matasa Masu Kirga Buhun Gero Suka Sa Jihar Kebbi A Idon Duniya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Wani dan siyasar daga jihar Legas mai suna Abayomi Sofumade, yana neman a bi masa hakkinsa a kan harbin da wani dan sanda ya yi masa a kafarsa a garin Itunpate cikin karamar hukumar Ikorodu da ke jihar Legas. Abayomi wanda aka fi sani da Bush, an dai kwantar da shi a asibiti tun lokacin da abun ya faru a ranar Litinin 8 ga watan Oktoba ta shekara 2018, ina aka bayyana cewa harsashi ya fasa masa kafa. Majiyarmu ta bayyana mana da cewan, shi dai Abayomi tsohon mai baiwa shugaban karamar hukumar Ikorodu shawara ta fannin watsa labarai da kuma tsare-tsare. Majiyarmu ta ce, ya bar gidansa da misalin karfe 8 na yamma inda ya tafi wajen mahaifiyarsa a garin Itunpate a nan ne lamarin ya rutsa da shi. Mutunim mai shekaru 36, ya ce, ya sami ‘yan sanda guda takwas suna jayayyan da wani dan acaba a bakin hanya, ya ba su shawara a kan su garzaya da lamarin zuwa ofis, kawai sai daya daga cikinsu ya harbe shi a kafansa.

Ya kara da cewa “na hau motana domin in je duba mahaifiyana, ina cikin tafiya sai na hadu da ‘yan sanda harma na gaishe su. Ban yi wani nisa ba, sai na hadu da wadansu ‘yan sanda guda takwas suna rikici da wani dan acaba, na matsa kusa da su, inda na tambaye su abin da yake faruwa. Sun gayamin cewa, wannan dan acaban ne ya fasa gilashin motan dan sanda.

“Na ga ‘yan sanda guda takwas suna jayayya da shi, sai na ba su shawara a kan su garzaya ofin domin su dai-daita lamarin. Ina shirin tafiya, sai daya daga cikin ‘yan sandan ya harbe ni. Na yi kokarin daukar hotun daya daga cikin su amma sai suka gudu. Bacin na samu taimako daga hannun mutane da kumu dan’uwana da suka kai ni asibiti ba, da na mutu saboda jinin da yake zuba a jikina.”

Labarai Masu Nasaba

Waiwayen Kanun Labarai Daga Litinin 15 Zuwa 18 Ga Sha’aban 1442 Bayan Hijira

’Yan Sanda Sun Gabatar Da Masu Manyan Laifuka 17 A Jos

Dan siyasan dai ya ce, dan sandar da ya harbe ni da kuma sauran ‘yan sandan duk suna aiki ne a ofishin ‘yan sanda da ke Igbogbo, ya kara da cewa, ya zayarci wani jami’a a ofis, inda ya bayyana masa cewa, ‘yan sandan dai suna gudanar da aikin ne ba bisa karida ba. Ya kara da cewa “lokacin da DPO da kuma DCO na garin Igbogbo suka ziyarce ni a asibiti, sun ce, suna cikin ofis a ranar amma ba su sami labarin faruwar lamarin ba. Sun kara da cewa, ba su san cewa ‘yan sandan sun fita ba, aikin da suka yi a wannan lokaci dai baya kan ka’ida.

“Zan gane dukkan ‘yan sandan, ina bukatar gwamnati ta shiga cikin lamarin, sannan kuma a hukunta su. Harsashi ya fasa min kafa, kuma bana tunanin cewa zan kowa yadda nike.”

Dan’uwar Abayomi, mai suna Femi Sofunmade ya ce, ya ji hayaniyar lamarin a bayan gidansu, amma bai san cewa dan’uwansa aka harba. Dan’uwan nasa mai shekaru 30 ya ce “ba mu san abin da yake faruwa ba, ba mu yi tunanin cewa Abayomi yana nan ba. Sai da wani makwabcinmu ya zo da gudu ya gaya mana cewa an harbi dan’uwanmu. “Na yi sauri na zo wajen inda na same shi cikin jini. ‘Yan sandan sun gudu bayan sun harbe shi.”

Mahaifiyar Abayomi, Modinat Sofumade ta bayyana cewa, lokacin da ta je ofishin ‘yan sandan domin kai kara, dan sandar da ya harbi yarona, ya musan ta lamarin. Mahaifiyar mai shekaru 75 ta ce “lokacin da ta ziyarci ofishin ‘yan sanda ranar da abun ya faru da dare, ta sami wani dan sanda a kanta, amma sai ya yi sauri ya fita daga ofis din. Dan sandan da ta samu a kan kantan da misalin karfe tara na dare, sai ya ce mata DPO baya nan. Ta sake dawowa washagari da misalin karfe takwas na safe. “Lokacin da ta sami DPO, sai ya kira dan sandan ya tambaye shi a kan lamarin, dan sandan ya musanta harbin da ya yi wa yarona, inda ya bayyana cewa, shi yana can majami’a lokacin da lamarin ya faru. Karya yake yi, ina so a hukunta shi domin ya zama izina ga sauran ‘yan sanda.”

Dan’uwan Abayomi, Yomi Shofumade ya bayyana cewa, sun kashe makudan kudaden wajen shan maganinsa, ya kara da cewa, DPO ofishin ‘yan sanda na Igbogbo ya yi alkawarin zai biya kudin maganisa amma bai biya ba. “Wannan ya nuna cewa tabas sun gudanar da aiki ba bisa ka’ida ba. ‘Yan sandan sun ta rokon mu a kan za su biya kudin maganin, amma haryanzu ba su biya ba,” inji dan’uwansa mai shekaru 50.

Lokacin da wakilinmu ya ziyarci asibitin, likitan da ke kula da Abayomi ya tabbatar masa da cewa lallai kafarsa ta karye. Likitan wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce “ya samu karaya a kafar, inda aka cire masa harsashi guda hudu a kafarsa, kuma a halin yanzu babu sauran harsashe a kafafunsa.

“Mutane suna ta bayyana cewa wai harbin shi ne ya sa kafan ta karye, amma ba shi ya kawo karayan ba. Idan harbin ya kawo wanna karaya, to ba zai wuce mako daya ba kuma mako biyu zai fara takawa, amma yanzu sai ya yi wata uku saboda karayan ya yi zurfi sosai.”

ADVERTISEMENT

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Legas ya bayyana cewa, babu wani lamarin harbi. Ya kara da cewa, Abayomi ya bukaci ya raba jayayya a tsakanin ‘yan sanda da kuma dan acaba kafin ya sami rauni. Ya ci gaba da cewa “abun da ya faru shi ne, ‘yan sanda suna cikin tafiya za su je aiki ta kusa da ‘yan acaba, sai daya daga cikin ‘yan acaban ya fasa musu gilashin moto. ‘Yan sandan suka kama shi, sai ‘yan acaba suka yi kokarin kubutar da shi daga hannun ‘yan sanda. Lokacin da ‘yan sanda suka ga cewa za a yi masu tawaye sai suka nemi taimako daga ofis inda aka turo masu jami’an tsaro. “An sami harbe-harbe tsakanin ‘yan sanda da ‘yan acaba, lokacin da dan siyasan ya ga lamarin ya yi kamari, sai ya isa wajen domin ya yi sulhu saboda ya san ‘yan sandan. A yayin rikincin, sai ‘yan acaban suka dauko sanda domin su buga wa ‘yan sanda sai suka sani dan siyasan a kafansa. “Babu wani harbin bindiga, ai ‘yan sanda ba ‘yan fashi ba ne da za su harbi shi don ya zo yin sulhu, me masa ba su harbi dan acaban da ya fasa masu gilashi mota ba.

“Amma duk da haka, kwamishinan ‘yan sandar jihar ya bayar da umurni a binciki lamarin.

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Shan Sigari Da Barasa Suna Kan Gaba Wajen Janyo Mutuwa A Duniya, Inji Kungiyar WHO

Next Post

Yadda Matasa Masu Kirga Buhun Gero Suka Sa Jihar Kebbi A Idon Duniya

Labarai Masu Nasaba

Labarai

Waiwayen Kanun Labarai Daga Litinin 15 Zuwa 18 Ga Sha’aban 1442 Bayan Hijira

by
1 year ago
0

...

’Yan Sanda Sun Gabatar Da Masu Manyan Laifuka 17 A Jos

by
3 years ago
0

...

Wata Mata Ta Kwace Jariri Daga Hannun Mahaifiyarsa A Ekiti

by
3 years ago
0

...

Benin: Wani Mutum Ya Kashe Surukansa Uku Saboda Tsananin Zalunci

by
3 years ago
0

...

Next Post
Yadda Matasa Masu Kirga Buhun Gero Suka Sa Jihar Kebbi A Idon Duniya

Yadda Matasa Masu Kirga Buhun Gero Suka Sa Jihar Kebbi A Idon Duniya

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: