Rabiu Ali Indabawa" />

Ana Amfani Da Bashin Da Gwamnati Ta Ciwo Yadda Ya Dace – Minista

Ministan sufurin jiragen kasa, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, yawan bashin da gwamnatin tarayya ta dukkan su ana amfani da su ta hanyar da ta dace, amma kuma yawan amso basukan zai iya sa a hana Nijeriya ciyo bashin nan gaba. Amaechi ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke zantawa da kwamitin duba yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da kuma wasu kamfanoni masu bayar da rance da zuba jari da kuma duba yadda ayyukan kwangiloli su ke gudana. Ministan ya kara da cewa, yana da kyau a ci gaba da gudanar da bincike kan yadda ake amso basuka, domin idan aka ci gaba a hana to manyan masana’antun masu zuba jari za su yi tsoron zuba jarinsu a Nijeriya, sakamakon basukan da ake bin kasar. Ya ci gaba da cewa, aikin karasa titin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan da kuma Kano zai samu cikas idan aka hana Nijeriya amso basussu ka a wannan lokaci.

Ya kuma shawarci shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ta ya ci gaba da gudanar da bincike a kan hanyoyin da ake bi da kuma ci gaba da za a samu wajen aikin da za a gudanar da basukan da ake amsowa a cikin kasar nan.
Majalisa tana ci gaba da gudanar da bincike kan yadda ake kashe kudaden gwamnati ba bisa ka’ida ba, inda ko a makon da ta gabata an gudanar da bincike a kan yadda miliyoyin kudade su ka salwanta a ma’aikatar bunkasa yankin Neja Dalta. Haka kuma majalisa ta sha alwashin bankado duk wani kudaden da aka kashi ba bisa ka’ida ba.

Exit mobile version