Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Ana Bada Bashin Korona Ne Bayan Awa 48 Da Cika Ka’ida – CBN

Published

on

Babban bankin Nijeriya CBN ya bayyana cewa, dukkan wadanda suka samin nasara amsan bashin Korona, za su tura bayanan asusun bankinsu ne ga sashen bayar da tallafin cutar Korona, sannan za a ba su wannan bashi bayan awanni 48 da mika bayanan asusunsu.

Daraktan yada labarain na CBN, Isaac Okorafor, shi ya bayyana hakan a cikin farkon wannan mako. A cewarsa, wadanda suke bai wannan bashi su ne, magidanta da kananan masana’antu wadanda cutar Korona ta shafa. Okoroafor ya shawarci dukkan wadanda suka sami nasarar su yi kokarin tura bayanan bankinsu ko su ziyarci bankin NIRSAL Microfinance Bank, domin mika bayanan bankinsu. Ya bayyana cewa, dukkan wanda ya samu nasara kuma bai sami bashin ba a cikin awo 48, to ya kai korafi ga hukumomin bankin CBN.

Okorafor ya kara da cewa, bankin ya bukaci wadanda suka samu cika ka’idojin bankin da su yi kokarin tura da bayanan bankinsu, domin a yanzu haka wasu sun fara samun kudaden ta asusun bankinsu.  Ya ce, babban bankin Nijeriya bai yi wasa ba wajen fara raba wa wadanda suka sami nasarar cimma ka’idodin amsan bashin. Kakakin babban bankin Nijeriyan, ya bukaci magidanta da kananan masana’antun da suka samu wannan bashi da su yi kokarin amfani da wannan kudade wajen inganta harkokin kasuwanci, domin kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.

A ranar 23 ga watan Maris ce, babban bankin Nijeriya ya aiwatar da ware naira biliyan 50, domin tallafa wa magidanda da kananan masana’antu wadanda cutar Korona ta dai-daita harkokin kasuwancinsu, domin yin amfani da wannan kudaden wajen farfado ka harkokin kasuwancinsu cikin gaggawa. A cikin ka’idojin da CBN ya gindaya har da nuna irin barnan da cutar Korona ta yi wa wadanda ke neman bashin tare da bayyana  kasuwancin da za su yi da wannan kudade idan amba su kudaden.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: