Abba Ibrahim Wada" />

Ana Barazanar Kashe Golan Liverpool

‘Yan sandan birnin Merseyside da ke garin Liberpool sun ce suna sane da sakonnin barazanar kisa da ake aike wa mai tsaron ragar Liberpool Loris Karius bayan wasan karshe na gasar zakarun Turai.

An rika tura wa dan kwallon na kasar Jamus, mai shekara 24, da iyalansa sakonnin barazana bayan kuskure biyu da ya yi wanda ya taimaka wa Real Madrid ta doke su da ci 3-1 a wasan na ranar Asabar.

Karius ya barke da kuka bayan an tashi daga wasan sannan kuma ya nemi afuwar magoya bayan kungiyar ta Liberpool yayin da su ma wasu daga cikin magoya bayan kungiuar suka rika daga masa hannu.

“Muna daukar irin wadannan sakonnin da ake wallafa wa a shafukan sada zumunta da muhimmanci. Za mu yi bincike kan dukkan laifukan da aka aikata,” a cewar ‘yan sandan.

Suka cigaba da cewa, “Jami’ai na sane da sakonnin barazana da aka tura ta shafukan sada zumunta kuma muna tunatar da masu amfani da wadannan shafuka cewa za a binciki duk wani al’amari da halayya mai kama da wannan.”

Mai tsaron ragar ne ya bai wa Karim Benzema kwallon farko da ya ci cikin sauki daga bisani Karius ya kasa tare kwallon da Gareth Bale ya buga daga nesa wacce ta bai wa Madrid damar saka kwallo ta uku da kuma lashe kofin.

Exit mobile version