Ana Bin Nijeriya Bashin Dala Biliyan 15.3 Na Kasar Waje

Kudade

Ofishin da ke kula da bashi na DMO ta ke a Babban Birnin Tarayyar Abuja ya bayyana cewa, bashin waje da ake bin kasar nan ya kai kimanin Dala biliyan 15.3 cikin tsawon shekara hudu da gwamnatin shugabancin Shugaba  Muhammadu Buhari.

Bashin ya kai kashi 148 cikin bisa dari  da ake bin kasar nan daga Dala biliyan 10.32 a watan Yunin 2015 zuwa Dala biliyan 25.61 a watan Maris na 2019.

A cewar ofishin, an ciwo bashin ne a karkashin gwamnatin Shugabn kasa Muhammadu Buhari wanda ta karbo bashin  na kasar waje.

Basussukan sun hadada na, Bankin duniya  Dala biliyan 2.71, na kasar Sin Dala bilayan 2.55, na bankin ciyar da nahiyar Afirka Dala biliyan 1.25, na Gidauniyar ADF Dala miliyan 834.18 na Gidauniyar aikin noma, Dala miliyan 176.19 na Bankin IDB Dala miliyan 15.51.

Sauran sun hada da, bashin Gidauniyat fitar da kaya kasar waje EDF dala miliyan 59.15, na Bankin tattalin arziki na Afirka ABEDA Dala miliyan 5.88 na kasar Japan Dala miliyan 74.63, na Bankin Edim da ke kasar Indiya Edim da kasar Jamus Dala miliyan198.25 sai kuma na Gidauniyar AFD da  ya kai Dala miliyan 366.07.

Farfesa Akpon Ekpo tsohon shugaban cibiyar kula da harkokin kudi da tattalin arziki a kasashen Yammacin Afirka ya sanar da cewa, bashin abin dubawa ne.

Exit mobile version