Ana Bincike A Kan Furta Kalaman Wariya Ga Dan Wasa Koulibaly

Koulibaly

Hukumar kwallon kafar Italiya ta bude bincike kan zargin nuna wariyar da magoya bayan Fiorentina suka yi wa mai tsaron bayan kungiyar kwallon kafa ta Napoli Kalidou Koulibaly yayin wasan kungiyoyin biyu a satin da ya gabata karkashin gasar Serie A. Baya ga Koulibaly ‘yan wasan Napoli irin su Bictor Osimhen da Frank Zambo dukkaninsu sun fuskanci kalaman wariyar da magoyan bayan na Fiorentina suka rika rerawa a wake bayan nasarar Napoli a karawar da kwallaye 2 da 1.

Kwamitin da hukumar kwallon kafar ta Italiya ta kafa zai yi tattaki zuwa Fiorentina domin fara bincike kan batun baya ga faya-fayan bidiyo da kwamitin zai yi amfani da su don tabbatar da zargin. Baya ga hukumar kwallon kafar, shi kansa ofishin babban mai shigar da kara na Italiya ya bude bincike kan batun, matakin da ke zuwa bayan tsanantar wariyar da ‘yan wasa bakar fata ke fuskanta a nahiyar ta Turai duk da ikirarin hukumomi na magance matsalar.

Dan wasan na Senegal wanda ya matukar fusata da abin da magoya bayan na Forentina suka yi masa har ta kai ga shigar da kara, ya bukaci zartas da hukuncin dakatarwar har abada ga duk wanda aka samu da laifin rera masa waken na nuna wariya. Wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram ya bayyana yadda magoya bayan ke kiransa da dan biri a duk lokacin da ya dauki kwallo, inda ya
ce irin wadannan mutane sam ba su cancanci ci gaba da kasancewa a filin wasanni ba.

Exit mobile version