Daga Ibrahim Muhammad
‘Yan Kasuwar kayan abinci na Duniya dake Dawanau sun koka da yanda kusan sama da shekaru ake ta jan kafa wajen gudanar da zaben shugabannin kungiyar ‘yan kasuwar wanda yanzu haka a sakamakon hakan ake tafiyar da kungiyar karkashin kwamitin riko da shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa ya kafa da kuma wani shugabancin da suka gudanar da zaben kungiyar da Alhaji Mustapha Mai Kalwa yake jagoranta.
Bincike da muka yi ya nuna cewa tsohon zababben shugaban kungiyar ‘yan kasuwar da ya jagoranci kungiyar har karo biyu Alhaji Mustapha Mai Kalwa daga baya ya sauka aka yi kantomonin riko daban-daban bisa sahalewa karamar hukumar Dawakin Tofa karkashin jagorancin Alhaji Ado Tambai Kwa ta kafa da yanzu Alhaji Sani Kwa yake a matsayin kwamitin riko ya dauki lokaci bai iya gudanar da shirya zaben da tunda farko aka ce zai gudanar a cikin watanni uku ba, wanda aka rika kara masa wa’adin da yanzu ya shafe sama da shekara daya.
Wata majiya, ta ce rashin tsayawa a gudanar da zaben shugabannin kasuwar ya doru ne a kan shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Hon. Ado Tambai Kwa wanda suke zargin ya yana nada kantoma na riko a kasuwar ne a matsayin dama ta mukamin siyasa da zai tafi dashi, ba tare da an gudanar da zabe ba, har zuwa lokacin gab da karshen wa’adin mulkinsa da yake a karo na biyu, sannan ne ake hasashen zai sa ayi zaben.