Abdullahi Sheme" />

Ana Cigaba Da Taya Gwamnatin Jihar Katsina Murnar Ceto ‘Yan Makarantar Kankara

‘Yan Makarantar Kankara

A makon da ya gabata ne ‘yan ta’adda suka yi dirar mikiya a wata makarantar kimiyya da fasaha ta kwanan dalibai dake Kankara, wani abin juya yi ya faru a makarantar inda yan ta’addar suka kwashe dalibai sama da yara 333 a daren ranar juma’ar da ta gabata.

A sanadiyyar haka ne yasa shuwagabannin al’umma da na kungiyoyi da masu fada aji   suke ta mika alhininsu tare da nuna jajantawarsu ga iyayen yara tare da gwamnatin Jihar Katsina a Karkashin Jagorancin Gwamnan Jihar Alhaji Aminu Bello Masari da masarautar Katsina a bisa Jagorancin Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman.

A cikin shuwagabannin akwai wani babban don siyasa na yankin shiyyar Funtuwa dake Jihar Katsina Alhaji Ibrahim Bala Mai Bulo inda ya kira taron manema labarai domin nuna damuwarsa akan lamarin inda ya fara da Kalmar Innalillahi daga nan ya ce yana kira ga iyayen yara da su dauki wannan lamari a matsayin kaddara kuma su yi hakuri don wannan lamari don wannan lamari ba su kadai ya shafa ba duk wani uba a ko ina yake a cikin fadin kasar nan wannan abu ya shafeshi, don haka tuni yasa aka cigaba da rokon Allah domin Allah ya bayyanasu cikin lokaci kuma cikin koshin lafiya, daga nan ya ce babu shakka gwamnan Jihar Alhaji Aminu Bello Masari ya kadu sosai kuma ya nuna damuwarshi akan lamarin domin daga jin labarin lamari ya hanzarta ya ziyarci makarantar kuma ya fara jawabi nan take ya kasa jawabin ya fashe da kuka saboda nuna tausayi da jimami akan lamarin domin rashin tsaro ya addabeshi kuma yarannan basu ji ba basu gani ba gasu kanana, daga nan ya ba iyayen yara hakuri kuma gwamnatin shi ta lashi takobin dawo da yaran cikin lokaci, kuma insha Allahu a raye. Daganan ya yi kira ga jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen kawo karshen lamarin.

A nashi jawabin shugaban kungiyar noman masara ta kasa Alhaji Bello Annur Funtuwa shima ya kira taron manema labarai a ofishin kungiyar dake Funtuwa inda ya nuna damuwarshi da tausayin shi musamman ganin yara ne kanana kuma basu san hawa ba balle sauka, wannan ba karamin tashin hankali bane don haka ya nuna tausayin shi ga yaran da iyayensu da ma sauran al’umma don haka ya yi kira ga dukkan musulman kasar nan dasu taya su addua’ar kubutar da yaran sannan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara nemo wasu dabarun kawo karshen rashin tsaron da ya addabi jihohin arewa.

A nashi jawabin shugaban kungiyar noman masara da sarrafata ta kasa reshen Jihar Katsina MAGPAMAN injiniya Magaji Ibrahim Dantankari shima ya yi kira ga iyayen yara da suyi hakuri wannan lamari basu kadai ya shafa ba, ya shafi dukkan wani mahaluki a kasar nan kuma ya ce tuni ‘yayan kungiyar na nan Jihar Katsina suka cigaba da yin addu’oin Allah ya kubutar da yaran cikin lokaci kuma a raye daganan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye wajen kawo karshen lamarin.

A nashi jawabin a lokacin da yake hira da manema labarai shugaban kungiyar Amana Association na jihohin arewa Alhaji Isah Balarabe Bilbis ya nuna alhininsa ga gwamnatin Jihar Katsina da kuma iyayen yara akan yadda ‘yan ta’adda suka dauki wasu daga cikin daliban makarantar kimiyya ta kwana dake Kankara.

Exit mobile version