Connect with us

Uncategorized

Ana Fuskantar Matsalar Samar Da Abinci A Sahel

Published

on

Shugaban hukumar Jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya, Mark Lowcock, ya yi gargadin cewar ana fuskantar matsalar samar da abinci a yankin Sahel wanda ke nuna karuwar mutanen dake fuskantar matsalar abinci mai gina jiki irin sa na farko tun bayan shekarar 2012.

Jami’in ya ce akalla kusan mutane milyan 6 ne ke shan wahala wajen samawa kan su abin da zasu ci a kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da Nijar da kuma Senegal, inda yara sama da milyan guda da rabi ke fama da tamowa.

Lowcock ya ce yanzu haka milyoyin mutane sun cinye dan abincin da suka yi tanadi, yayin da wasu suka fara rage yawan abincin da suke ci a rana da kuma janye yaran su daga makarantu.

Jami’in ya kuma ce matsalar rashin abincin ya karu da kashi 50, yayin da kowanne yaro guda daga yara 6 ke bukatar kulawa ta musamman.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: