Ma’aikatan agajin gaggawa a lardin Hebei na arewacin kasar Sin da ambaliya ta aukawa, sun karfafa kokarin gyara tituna da gadojin da suka lalace, domin tabbatar da isar da kayayyakin agaji da na aikin ceto ba tare da tangarda ba.
Ruwan sama dake ci gaba da sauka a kwanakin baya-bayan nan ya haifar da ambaliya da zaftarewar kasa a fadin lardin, lamarin da ya rutsa da gundumomi da dama.
Zuwa safiyar jiya Asabar, an dawo da zirga-zirga a sassan tituna 961 dake fadin lardin Hebei. (Fa’iza Mustapha)