Bello Hamza" />

Ana Horar Da Masu Bautar Kasa 1,500 Da Aka Tura Jihar Borno A Katsina

Daga Bello Hamza

Masu bautar kasa 1500 da aka tura yi wa kasa hidima jihar Borno suke karbar horansu a jihar Katsina a halin yanzu.

Da yake jawabi a yayin bukin ratsar dasu a makaratar “Cibil Defence College” dake Katsina,  in Katsina, gwamnan jihar Borno Kashim Ibrahim ya bukaci ‘yan yi wa kasa hidimar su yi aiki tukuru wajen aikin gina kasa hidima.

Ya ce, tsarin NYSC ya tanadi samar da matasa masu kishin kasa da aiki tukuru da kuma kasancewa masu kawo canji na gari a cikin alumma, saboda haka gwamnati ta dauke shi da mahimamanci a fagen raya kasa.

‘Gwamnatin jihar Borno ta dauki matakan farfado da kuma gyare gyaren wyraren da aiyukan ta’addancin Boko Haram ya haiyar a sassasan jihar” inji shi.

Tun da farko, shugaban shirin NYSC a jihar, Rabiu Aminu, ya bukaci masu guji duk wani abu da zai bata musu suna da kawo wa aikin da suke yi cikas a tsawon lokacin da zasu yi na yiwa kasa hidima, ya kuma bukaci su shiga dukkan aiyukan da aka tanada na kawo ci gaban al’umma a yayin zaman su a jihar.

 

Exit mobile version