Connect with us

RAHOTANNI

Ana Inganta Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Don Tabbatar Da Kyakkyawar Makoma Ta Bai Daya

Published

on

A gun bikin bude taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka (FOCAC) da aka gudanar a ranar Litinin din da ta gabata da yamma a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, shugaban kasar Sin ya gabatar da jawabi mai taken “hada kan juna tare da sa kaimin ci gaban juna”, inda ya gabatar da cewa, nan da shekaru uku masu zuwa, kasar Sin za ta aiwatar da wasu shirye-shirye takwas, a kokarin kara tabbatar da kyakkyawar makomar Sin da kasashen Afirka ta bai daya a fannonin da suka shafi bunkasa masana’antu, da ababen more rayuwa, da saukaka harkokin cinikayya, da bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, da inganta kwarewar kasashen, da kiwon lafiya, da musayar al’adu da kuma tsaro. Kasar Sin dai ta gabatar da matakan ne bisa ga makomar Sin da Afirka, wadanda suka tsara taswirar bunkasa huldar da ke tsakanin sassan biyu a sabon zamanin da ake ciki.

A yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara kasashen Afirka a shekaru biyar da suka wuce, ya bayyana huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka, a matsayin “kasashen da ke da makomar bai daya”, kuma hakan ya faru ne a sakamakon tarihi, da aiki, da kuma moriya ta bai daya a tsakanin sassan biyu, wato tun tuni sassan biyu na ma’amala da juna ta fannoni daban daban.

Tun bayan da aka kafa dandalin FOCAC a shekarar 2000, yawan ciniki da ke tsakanin sassan biyu ya karu da sau 17, a yayin da yawan jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen Afirka ya karu sama da sau 100, kuma hadin gwiwar samun moriyar juna, da tabbatar da ci gaban juna, sun zama burin da ake neman cimmawa, wajen raya huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka cikin karni na 21.

A halin yanzu, kasar Sin na kara kawo sauye-sauye a gida, da habaka bude kofarta ga kasashen waje, a wani kokarin na neman cimma burin samun bunkasuwa da aka tsara, a cikin muhimmin rahoto na babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19. Ita kuwa Afirka, domin cimma burinta na raya masana’antu, da sana’o’i daban-daban, gami da dunkulewar dukkanin nahiyar baki daya, ta kuma tsara muradun da take son cimmawa zuwa shekara ta 2063. Amma a halin yanzu a duk fadin duniya, ana fuskantar manyan sauye-sauye da canje-canje, kana ana kara samun abubuwa masu haifar da rashin tabbas, da rashin kwanciyar hankali.

A irin halin da ake ciki, Sin wadda ta kasance kasar dake tasowa mafi girma a duniya, da Afirka wadda aka fi samun kasashen dake tasowa a duniya, dukkansu suna da niyya, gami da bukatu na karfafa hadin-gwiwa tsakaninsu. Kana akwai babban nauyin dake wuyansu na kare tsarin yin cinikayya cikin ’yanci, wanda ke kunshe da bangarori daba-daban a duk duniya. Don haka, inganta kafa makomar bil’adama ta bai daya ta Sin da Afirka, da kuma hada bunkasuwar kasar Sin tare da ci gaban nahiyar Afirka, sun zama abun da ya kamata a yi a wannan halin da ake ciki.

A cikin jawabin da ya gabatar, shugaba Xi Jinping ya sake jaddada cewa, yayin da kasar Sin ke kokarin karfafa hadin-gwiwa da kasashen Afirka, ya ce sam ba za ta yi abubuwan da ba su dace ba, yana mai cewa ba za ta tsoma baki cikin yadda kasashen Afirka ke kokarin neman samun bunkasuwa ba, kuma, ba za ta yi shiga sharo ba shanu cikin harkokin cikin gidan kasashen Afirka ba, kana, ba za ta tilastawa kasashen Afirka amincewa da dukkanin ra’ayoyinta ba, kana kuma, ba za ta gindaya wani sharadin siyasa kan kasashen ba, a yayin da take samar masu da tallafi.

Haka zalika, kasar Sin ba za ta nemi samun moriya ita kadai ba, yayin da take kokarin zuba jari a kasashen Afirka. Wannan shi ne matsayin da gwamnatin kasar Sin ta dade tana tsayawa a kai, yayin take yin hadin-kai da kasashen Afirka, abun da ya dace da wasu manyan manufofin da shugaba Xi Jinping ya gabatar don karfafa zumunci da kasashen Afirka, wato nuna gaskiya da sahihanci, da amincewar juna tsakanin Sin da Afirka. Wannan zai taimaka ga karfafa hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da neman samun moriya, da cimma alfanu tare, da kuma raya al’adu da inganta tsaro tare a tsakaninsu.

Domin cimma wannan buri, shugaba Xi ya gabatar da cewa, Sin za ta dauki manyan matakai 8, da kuma baiwa kasashen Afirka tallafin kudi na dalar Amurka biliyan 60 ta hanyar ba da taimako da gwamnati za ta yi, da tattara kudi, da hukumomin kudi da kamfanoni za su yi. Wannan ne mataki na nan gaba, na kara ingancin hadin kai tsakanin Sin da Afirka bisa tushen manufofi, da matakai 8, na inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka da aka gabatar a taron koli da aka shirya a shekarar 2006 a birnin Beijing, da muhimman shirye-shiryen hadin kai 10 a tsakanin Sin da Afirka, wadanda aka gabatar a taron koli da aka shirya a shekarar 2015 a Johannesburg. Wannan shirin na da halin musamman a fannoni guda uku.

Da farko, Tsayawa kan mai da moriyar jama’ar Sin da Afirka a gaban komai. A yayin jawabinsa, shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata a mai da jin dadin jama’a a muhimmin matsayi wajen raya dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. Ya kamata a samar da hakikanan nasarori ga jama’ar bangarorin biyu. Wadannan manyan matakai 8 na hade da nuna goyon baya ga Afirka, wajen tabbatar da samun isasshen abinci kafin shekarar 2030, da kyautata ayyukan kiwon lafiya guda 50, da aiwatar da ayyukan kulawa da mata da kananan yara, da aiwatar da ayyuka 50 na al’adu da wasannin motsa jiki da yawon shakatawa, da kuma ayyukan ba da tallafi a fannin tsaro guda 50 da dai sauransu. Dukkansu sun nuna ra’ayin na inganta hadin kai domin jin dadin jama’ar Sin da Afirka.

Na biyu, za a kara mai da hankali kan kara karfafa karfin samun ci gaba bisa dogaro da kai. Sinawa suna ganin cewa, hanya mafi dacewa yayin da ake samarwa saura tallafi ita ce, a koyar da su yadda ake kamun kifi a maimakon ba su kifi kai tsaye, wato ya dace a samar da tallafin kayayyaki, a sa’i daya kuma a taimaka wajen samun ci gaba bisa dogaro da kai. Daya daga cikin matakai guda takwas da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar shi ne, kara karfin samun ci gaba bisa dogaro da kai, misali samarwa samarin kasashen Afirka damammakin koyon sana’o’i, da samar da taimako kan aikin kafa cibiyar hadin gwiwar kirkire-kirkire dake tsakanin Sin da Afirka, da kuma ba da jagoranci gare su wajen samun ci gaba. Makasudin wannan yunkuri shi ne horas da isassun kwararru ga kasashen Afirka, tare kuma da taimakawa kasashen nahiyar Afirka, domin su cimma burin samun ci gaba bisa dogaro da karfin kansu.

Na uku, kara karfafa aikin tsara tsare-tsaren raya kasa. A cikin shekaru 3 da suka gabata, kasar Sin tana tabbatar da shirye-shiryen raya kasashen Afirka guda goma lami lafiya. Haka kuma an riga an samu kudaden da ake bukata, ko tsara shirin da abin ya shafa, kana yayin da ake gudanar da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, an riga an kyautata hanyarsa, wato daga aikin da ake yi karkashin jarorancin gwamnati, zuwa aikin da ake yi bisa bukatun kasuwa. Wajen hadin gwiwar cinikayyar hajoji kuwa, an riga an samu ci gaba, har ana gudanar da hadin gwiwa wajen samar da kayayyaki tsakanin sassan biyu. Ban da haka kuma, ana kara mai da hankali kan aikin zuba jari a maimakon gudanar da aikin gini a kasashen Afirka.

Matakai guda takwas da Xi ya gabatar za su taimaka wajen ingiza aikin aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, da ajandar raya kasa ta AU nan da shekarar 2063, da ajandar samun dauwamammen ci gaba ta MDD nan da shekarar 2030, da tsare-tsaren raya kasa na kasashen Afirka daban daban, ta hanyoyin sa kaimi kan aikin samar da kayayyaki, da kyautata aikin amfani da kayayyakin da ake bukata, da saukaka sharadin gudanar da cinikayya, da samun ci gaba, tare da kiyaye muhalli da sauransu, wanda ta haka ne za a cimma burin bude wani sabon shafin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, musamman ma wajen samun ci gaban tattalin arziki a sabon zamanin da ake ciki, tare kuma da samun moriyar juna ta hanyar yin hadin gwiwa yadda ya kamata.

Ya zuwa yanzu dai, dandalin FOCAC ya kafu har tsawon shekaru 18, wanda ya yi watsi da ra’ayin yin takara ba tare da hadin kai ba, da samu wata sabuwar hanyar hadin gwiwa don cimma moriyar juna, hakan ya zama wani abun koyi yayin da ake kokarin raya makomar bil adama ta bai daya. Kamar yadda shugaban kasar Gabon Ali-Ben Bongo Ondimba ya ce, “dalilin da ya sa dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka ta samu nasara shi ne, sabo da sun nuna sahihanci da amincewa, da ma girmamawa ga juna.” Yau, hadin kan Sin da Afirka na kan wani sabon mataki, yadda za su tinkari batun zaman lafiya da bunkasuwa domin neman samun ci gaba tare, ba shakka wani zabi bai daya ne, na bangarorin biyu.  (Lubabatu, Murtala, Bilkisu, Jamilah, Kande)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: