CRI Hausa" />

Ana Mutunta Al’adun Kananan Kabila A Jihar Xinjiang

Abdulim Jumai mai shekaru 50 da haifuwa, yana aiki a wani kamfanin samar da siminti dake gundumar Luopu dake yankin Hotan na jihar Xinjiang mai cin gashin kanta. Yana aiki a kamfanoni uku bi da bi, wannan kamfani mai samar da siminti yana kusa da gidansa, shi ya sa ya zabe shi. Ya ce, ya kwashe shekaru fiye da goma yana aiki a kamfanoni daban-daban, amma ana mutunta al’adunsa da kuma addininsa.
Abdulim Jumai yana jin dadin yanayin kamfanoninsa a yanzu. Ya ce, ana mutunta al’adun kananan kabilu, musamman ma game da wasu manyan bukukuwa, kamar karamar Sallah da babbar Sallah, inda kamfanin ke samarwa duk ma’aikaci kudin Sin yuan 800 zuwa 1000 don sayen naman sa da rago. Ban da wannan kuma, kamfanin yana gudanar da manyan bukukuwa don murnar bikin addini.
Ya kara da cewa, yana more rayuwa a lokacin hutu, kamfanin ba zai tsomo baki cikin zaman rayuwarsa ba, ciki hadda al’adun aure da jana’iza da dai sauransu. (Amina Xu)

Exit mobile version