Masana sun bayyana cewa, Lemun zaki ya samo asali ne daga kasaahen Indiya, China a nahiyar Asiya, har Ila yau, Nijeriya ma ba a barta a baya ba wajen nomansa, musamman ganin cewa, ana samun dimbin riba daga fannin.
Bukatar da ake da ita ta Lemun zaki na kara karuwa a cikin al’umna, inda hakan ya sa ake da karin bukatarsa kuma wannan babbar dama ce ga masu son su zuba jarinsu a fannin Ana yin noman Lemun zaki har zuwa karshen shekara, an kuma fi samun amfaninsa mai yawa daga watan Afirilu zuwa watan Mayu, har Ila yau, Lemun zaki na dauke da sinadaran Vitamin C ana kuma sarrafa shi zuwa nau’ukan kayan sha da dama ko kuma a sha shi zalla.
Bugu da kari, Nijeriya ta kasance ta daya a nahiyar Afirka wajen nomansa, inda kasar Masar na bi mata sai kuma wasu kasashe tara da su ka biyo baya a duniya.
Jihohin da suka fi nomansa su ne Benuwai, Nassarawa, Kogi, Taraba, Kaduna, Kwara, Osun, Ogun, Edo, Ebonyi, Delta, Imo, Oyo da kuma Osun.
Gyaran Gona: Ana bukatar manomin Lemun zaki kafin ya fara komai, ya tabbatar da ya gyara gonar da zai shuka shi, tare da zuba wa takin zamani.
Lokacin Yin Shuka: Ana son a yi rami mai zurfin santi mita 606, musaman don a bayar da sarin da ya kai mita 3.3., musamman don amfanin ya yi saurin girma.
Loakcin Da Yake Kai Munzalin Nuna: Lemun zaki na kai wa tsawon lokaci kafin ya fara yin ‘ya’ya, haka renon nomansa, na kai wa daga shekara 8 zuwa 13, haka manominsa zai iya sayen Irin nomansa daga gun mutane da ke renon Irin ko kuma ya rene su da kansa.
Yanayin Da Lemun Zaki Yafi Bukata: Lemon zaki ya fi son yanayi mai sauki, musamman don kare shi daga harbin cuttuka tare da kuma bayar da irin kalar da ake bukata.
Yanayin da ya fi dace wa shi ne kimain ma’aunin yanyi 13°C zuwa mau’nin yanayi to 38°C ko kuma ma’unin yanayin da ya kai daga 25°C zuwa ma’unin yanyi 35°C.
Zuba Takin Zamani: Ana bukatar a yi amfani da takin zamani samfarin NPK, inda ake son a zuba takin sau biyu ko sau uku a shekara.
Yin Ban Ruwa: Ana son ayi masa ban ruwa sosai, amma ba a son yin ban ruwan ya yi yawa matuka.
Kare Shi Daga Harbin Kwari Da Cututtuka: Akwai kwari da kuma cututtukan da ke yiwa Lemon zaki illa a saboda haka, ana son manominsa ya tabbatar ya tanadi magungunan kashe kwari da na cuttukan.
Lokacin Yin Girbi: Amfanin sa na fara nuna ne daga shekaru uku daga lokacin da aka shuka shi, inda kuma ya ke kammala nuna gaba daya bayan ya kai shekaru goma haka a kadada daya, ana iya sumun tan daga goma zuwa sha biyu.
Hada-hadar Kasuwancinsa: Manominsa zai iya sayar da shi a kasuwa ko kuma a manyan