Connect with us

LABARAI

Ana Samun Karin Fahintar Juna Tsakanin Yarbawa da Hausawan Jihar Legas

Published

on

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar bakin saman shedi Agege ta JiharLegas Alhaji Saidu Magaji Milas ya bayyana cewar ahalin yanzu babu irin mu’amullar da al umar hausawa da na yarabawa mazauna Jihar Legas basu yi ajunansu saboda samun wanzuwar zaman lafiya a tsakaninsu inji shi, hasalima akwai aurataiya da suke yi a tsakanin junsin guda biyu.

Saidu Magaji Milas ya fadi haka ne a unguwarAagege a lokacin da wadannan junsi guda biyu Yarabawa da na Hausawa suka zama tsintsiya madaurinki daya kuma suka zama kamar danjuma da dan jummai a wajen gudanar da shagulgulan wannan sallar data gabata, ya ci gaba da cewa, a yanzu haka ma in kaje zango wurin da Hausawa suka fara zama da suka shigo Agege baka iya gane wanene Bahaushe wanene Bayarabe a wajen hudda da junansu da kuma alamuran da suka shafirRayuwarsu.

Ya kuma kara fa cewa, an samu wanzuwar zaman lafiya tsakanin malam Bahaushe da Bayarabe sannan kuma ya cigaba da zaiyana ci gaban da malam Bahaushe ya samu a Jihar Legas ya ce, bari ya yi misali da unguwarsa ta Agege, Bahaushe y agaji abubuwa guda uku na farko neman zaman lafiya na biyu rikon addininsa na uku rike sana’ar neman abincinsa sannan kuma ya kara da cewa, a unguwar Agege duk inda kaga gida mai kyau a Agege na malam Bahaushe ne ya ce, wannan ba karamin ci gaba bane a wurin malam Bahaushe da yake zama a Jihar Legas.

Shugaban da ya koma kan siyasar Nijeriya a halin yanzu kuwa, ya ci gaba da cewa ne, abu biyu ko kuma uku suka bata siyasar Nijeriya ahalin yanzu, na farko a shekarun baya kowane irin mukami kake nema sai yanda jami’yya tayi da kai amma idan ka kalli siyasar yanzu ba haka bane sai kaga wai karamar kujera ta kansila idan aka zabeka a matsayin kansila da shugaban jami’yya na ward da shugabannin jami’yya na akwatuna na unguwar ni da sauran masu mukani a jami’yyar na wannan yanki gidan wurin taruwar ‘yan maula.

A kan haka yake bada shawara su gyara siyasar arewacin Nijeriya ya kara da cewar sai kaga an zabi mutun amatsayin Gwamna a waccan jami’yya kuma yana so yakoma wata jami’yyar baya tunanin cewar a waccan jami’yyar aka zabe shi sai ya koma can kai tsaye ba tare da ya ajiye mukuminsa ba,ya kamata a yi wani abu akan wannan.

 
Advertisement

labarai