Ana Shan Kwaya Fiye Da Kima A Sansanin ’Yan Gudun Hijira –NDLEA

Shugaban hukumar NDLEA na jihar Borno, Joseph Iweanunawa ya nuna damuwarsa a kan yawan amfani da muggan kwayoyi da ake yi a sansanin ‘yan gudun Hijira na Maiduguri.

Kwamanda Joseph ya kuma nuna takaicinsa kan yadda sansanin gudun hijiran ya zama wata cibiyan sha da safarar kwayoyin, a kwai kuma wasu bata garin jami’an tsaron dake taimaka wa ‘yangudun hijiran safaran kwayoyin ba tare da sun sani ba.

“Bincikenmu ya nuna mana cewa, wasu jami’an tsaron sun zama jakadun sayar da kwayoyi ga ‘yan gudun hijiran da suka zama ‘yan kwaya saboda halin da suka shiga ciki na tashin hankai”

“Abin takaicin shine a takure muke ba zamu iya daukan mataki a kan su ba saboda matsayinsu na ‘yan gudun hijira duk da dokan nan ta Kampala” in ji shi.

Ya kuma bayyana wa manema labarai cewa, lamarin na tayar masa da hankali kuma lallai zai dauki matakin da ya dace a kan jami’an tsaron da ke amfani da kayan sarkinsu wajen safarar kwayoyi domin hakan ya zama darasi ga sauran masu kayan sarki. Ya ce, a shekarar 2017 hukumar ta kafa wani kwamiti domin ya lura da yawan safara da amfani da miyagun kwayoyi an kuma samu hadin kai daga sauran bangaren gwamnati da ta dace domin samun cikakken nasarar aikin. Ya ce, an kama mutane 132 da laifuffukan hurda da kwayoyi daban-daban musamman a ciki garin Maiduguri, an kama kilo gram 7.334 da Grams 3.8 na maganin tari mai dauke da sinadari Kodin suna nan an ajiye domin gabatar wa a matsayin shaida in an gabatar da su gaban kotu.

Sauran kwayoyin da aka kama sun hada da kilo gram 17.865 na ganyen Wiwi da Kilo grams 23.820 na kwayar Tramadol da kilo gram 4.018 da kwayar Diazepam da Kilo gram 582 na Edol da Kilo gram 232.6 na kwayar Kuinine da kuma Gram 195.6 na kwayar Ergometrine. Dukkan wadanda aka kama mazaje ne an kuma kama su da kwayar Pentazocine gram 111 da Amitriptyline gram 74.6 da maganin tari mai dauke da sinadarin kodin gram 35.85 da Rohypnol grams 235.6 da pentobarbital grams 16.4 da kuma co-codamol grams 193.5. Da yake mayar da martini a kan halin da hukumar NDLEA ke ciki, Kwamishinan Shari’a na jihar Barrister Kaka Shehu ya ce, abin da ya faru shi ne bayan kafa kwamitin da aka shirya zai fuskanci masu safara da shan miyagun kwayoyi ne hukumar zartaswa jihar ta yi wa wasu Daraktocin dake cikin kwamitin canjin aiki abin da ya yi mummunan illa ga yakin da ake yi da miyagun kwayoyin a Maiduguri da kewaye duk da yaki da ta’addanci da a ke fuskanta a jihar da sauran makwabtan jihohi.

“Lokacin da aka fara yakin Boko Haram aikin ya yi sanyi, mun dan tsaya domin tsira da rayukanmu, bayan an dan samu zaman lafiya musamman a cikin garin Maiduguri kwamitin ya ci gaba da aiki har na basu lauyan da zai yi aiki tare da su, amma a halin yanzu ba zan iya ce maka ga halin da ake ciki ba “ in ji shi

Wasu ‘yan Boko haram din da suka tuba sun bayyana cewa, yawancin ‘yan harin kunan bakin waken da ake samu sai an basu kwaya da allurorin da zai gusar musu da hankali ta yadda zasu tafi su tarwatsa kansu da nufin cika alkawarin masu gidansu.

Dukkan bangarori 3 na kungiyar Boko Haram na amfani ne da kwayoyi wajen kangarar da magoya bayansu musamman wadanda suka bayar da kansu a matsayin a yi kunan bakin wake dasu a wurare daban-daban har da ofoshin NDLEA. Ofishin Hukumar NDLEA da aka tarwatsa kwanakin baya na tsanananin bukatar gyara in har ana son ta zauna da gindinta har ma ta iya yaki da miyagun kwayoyi a wurare daban-daban musamman sansanin gudun hijira

 

Exit mobile version