Abdulazeez Kabir Muhammad" />

Ana Shigo Da Buhun Shinkafa Miliyan 200 Nijeriya Kullum Ta Haramtacciyar Hanya

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa ana shigo da buhuhunan shinkafa miliyan 20 kasar Nijeriya a kullum ta haramtacciyar hanya. Babban manajan Labana Rice Mills, wani kamfani na asali mai noma da sarrafa shinkafa a jihar Kebbi, Abdullahi Zuru yayi korafi akan cigaba da ake samu wajen shigowa da shinkafa Nijeriya ta haramtattun hanyoyi.
 A wata ganawa da Zuru ya yi da manema labarai a Birnin Kebbi, yace hakan ya zamo barazana ga shirin ba da rance wacce babban bankin Nijeriya (CBN) ta kaddamar don tabbatar da noman shinkafa a kasar.
An rawaito cewa Zuru yace kungiyar manoman shinkafa na Nijeriya (RIFAAN) ta gudanar da bincike tsakanin watan Fabrairu zuwa Maris na wannan shekarar, binciken ya kuma nuna cewa fiye da buhunan shinkafa miliyan 20 ne ake shigowa dasu Nijeriya ta haramtattu hanyoyi da iyaka daban daban.
A watan Disamban da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kamfanin shinkafa na miliyoyin nairori na wani dan Indiya. Wakilin ya bada tabbacin cewa ana aiki don ganin an inganta yawan abunda ake samu zuwa tan 500 a watan Yuli.
Exit mobile version