Connect with us

KASUWANCI

Ana Shirin Taimaka Wa Manoman Nijeriya Shiga Kasuwannin Dubai

Published

on

Wani Kamfanin tuntuba dake sarrafa na’orori fahasa na zamani mai suna, , Crenob8 dake a yankin Gabas ta Yamma da kuma nahiyar Afrika, ya nuna aniyarsa ta samar da Kasuwa a tsa kanin Manoaman Nijeriya da kua masu sayen kaya a kKasuwannin dake Dubai da sauran sassan dake cikin nahiyar Afirka.
A bisa tsarin wannan kirkirar, Kamfanin na Crenob8, ya sanar da ha kan ne a ranar goma ga watan Okutoba a matsayin ranar da zai tara Manoman a taron masu fitar da kaya kasar waje, inda zai gana da da Manoma a taron mai taken,’ Makomar kaasuwancin amfanin Gona’.
A taron kaddamawar data gudana a jihar Legas Kamfanin ya sanar da cewar, zai sada manyan masu sarrafa kaya da masu saye dake Gabas ta Tsakiya.
Sanarwar takara da cewar, masu ruwa da tsaki daga Afirka dana Cibiyar hadin kai ta Gulf, zasu iso wurin taron na kwanan daya don yin hadaka da yadda za’a ciyar da amfanin Gona a nahiyar ta Afirka.
Ta kuma yi nuni da cewar, babban abin mahimmanci shine, Manoman na Nahiyar Afirka da wadanda zasu halarci taron da wadnda zasu baje koli da kuma wakilai, zasu amfani da damar taron yadda Manoman zasu shiga Kasuwannin na Dubai da kuma sauran kasashen.
Taron za a gudanar da shi ne da hadkar Kamfanin zirga-zirgar matafiya da ake kira Geo da kuma sauran masu ruwa da tsaki.
Masu shirya taron daga MTFC, Bola Oyedele, wanda ya samu wakilicin Gbemi Ajide na sashen tuntuba na kasauwanci daga Kamfanin Creanob8 ya ci, MTFC ya mayar da hankali ne a kan dukkan manya da kanana Manoma wajen samar da dala biliyan 100 a Kasuwar ta Dubai.
Bugu da kari, masu ruwa da tsaki da suka fito daga sauran Bankin Manona, Ma’aikatar Masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Ma’ikatar Noma da kuma Masana’antu masu zaman kansu kamar na Farmcrowdy da AFED, zasu taimakawa Manoman a kan yadda zasu fitar da amfanin Nomansu zuwa Daular Larabawa.
A nashi bangaren, Babban Jami’i na sashen Kudi da kiyaye asara na Bankin Manoma Yarima Niyi Akenzua, ya bayyana cewar MTFC abune mai kayu wanda kuma ya nkamata aci gaba da yinsa don a cimma manufar da aka sanya a gaba na sada Manoman kasar na n da kasuwar da Daular Larabwa.
Shugaban Cibiyar baje koli da Masana’antu na jihar Legas Mista Babatunde Ruwase, ya yi nuni da cewar, MTFC zai kara bayar da kwarin Gwaiwa da masu ruwa da tsaki da dama don su zuba jari a fannin Noma da kuma taimakawa wajen dankon kasuwanci da Daular ta Laarabawa.
Shi kuwa Babban Jami’i na Farmcrowdy, Onyeka Akumah, ya yaba wa shirin na MTFC, inda ya yi nuni da cewar, taron zai taimaka wa masu ruwa da tsaki sosai dake nahiyar Afirka.
Ya kara da cewar, ha kan zai basu damar daukar mataki don kasancewa a karkashin inuwa guda, inda dukkan fanonin za su samu damar tattaunawa a kan fanin aikin Noma da kuma samar da mafita yadda dukkansu za su amfana da juna.
Shima da yake jinjina wa shirin manajan musayar kayayyaki na AFED dake a kasar nan, Ayodeji Balogun ya ce, AFED taji dadin yin hadaka da shirin na MTFC ganin cewar ha kan zai samar da kasuwar sayar da amfanin Gona tsakain Nijeriya da Gabas ta Tsakiya.
Har ila yau, shirin na MTFC Ma’aikatar Gona ta jihar Legas, Kungiyar Kasuwanci da Masana’antu, Ma’adanai da Noma da Bnakin fitar da kaya zuwa kasar waje da sauransu duk sunyi na’am da shirin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: