Mustapha Abdullahi" />

Ana Son Haifar Da Rigima Tsakanin Fulani Da Al’ummar Hausawa Ne -Bayero

Mataimakin shugaban kungiyar matasan al’ummar Fulani ta kasa, Alhaji Abdulkarim Bayero ya bayyana wa manema labarai cewa sakamakon irin kyakkyawan binciken da suka gudanar, ya tabbatar masu cewa ana yi wa jama’ar yankin Arewacin Nijeriya tarko ne ta yadda za a lalata yankin baki daya.

Ita dai kungiyar mai suna ‘Fulbe Ummiobe Sukabe Debelopment Association  FASADAN)’ an samar da ita ne domin ciyar da kasa gaba, musamman ta fuskar wayar wa da daukacin al’umma kai a game da abubuwan da suka shafi ci gaban rayuwa baki daya.

Bayero ya ci gaba da cewa, suna nan za su fara aikin zuwa wurare domin wayar wa ‘yan uwa Fulani da kai a game da abin da ya shafi harkokin rayuwa ta fuskar Ilimi, al’amuran rayuwa baki daya.

“Mun gano wani al’amarin da a halin yanzu sai mun tashi tsaye mu jama’ar Arewacin Nijeriya saboda irin yadda ake kokarin wargaza yankin Arewa, amma hakan ba zai samu ba sai an hada fitina tsakanin al’ummar Fulani da Hausawan Arewa, kuma Allah ya taimake mu mun fahimci hakan, shi ya sa muke fadakar da jama’a”, in ji Bayero.

Ya ci gaba da bayanin cewa “za mu fara shirin fadakarwa ga al’ummar Fulani domin su fahimci yadda al’amuran suke tafiya a kasa. Muna kira ga gwamnatin tarayya da sauran jihohin kasar nan da su sani cewa babu inda babu batagari a cikin al’umma, don haka ya dace a dauki muhimmin abin da zai kawo warwarewar matsaloli a kasa. Kasancewa akwai masu matsala ‘yan kalilan a cikin Fulani, ba shi ne ke alamta cewa duk Fulani suna da matsala ba.

Exit mobile version