Shugaban hukumar qwallon qafa ta duniya FIFA, Gianni Infantino ya gamu da kakkausar suka bayan kalamansa na qoqarin kare yunqurin mayar da gasar cin kofin duniya duk bayan shekaru biyu da ke cewa matakin zai ceto dubban rayukan ‘yan ciranin Afrika da ke mutuwa a kowacce rana a qoqarin shiga Turai.
Infantino ya ce manufar mayar da gasar duk bayan shekaru biyu ba wai za ta bayar da wasu kudade ko kuma tallafi ga ‘yan ciranin ba, amma za ta basu damar halartar wasannin gasar da zai dauke hankulansu daga qoqarin shiga Turai domin samun ingantacciyar rayuwa.
Acewar sa qoqarin inganta gasar ta cin kofin duniya zai fi amfanar da Afrikawa fiye da kowanne yanki la’akari da yadda suke rasa damar ganin wasannin gwanaye sabanin takwarorinsu na Turai da ke kallon manyan wasanni a kowanne mako.
Sai dai bayan kakkausar suka kan wannan kalamai daga qungiyoyin kare haqqin dan’adam da daidaikun fitattun ‘yan wasa da ke qalubalantar shirin mayar da gasar duk bayan shekaru 2, Infantino ya ce an yi wa kalaman nasa bahaguwar fahimta.
Shirin mayar da gasar cin kofin duniya duk bayan shekaru biyu sabanin bayan shekaru hudu da aka saba tun shekara ta 1930 ya gaza samun goyon bayan hukumomin qwallon qafar Turai da na Kudancin Afrika, haka zalika manyan qungiyoyi, sai dai wasu bayanai na cewa qasashen Afrika 54 na goyon bayan yunqurin na FIFA a asirce.