Ana Wata Ga Wata: Yau Kungiyar Malamai Za Ta Sa Zare Da el-Rufai

Ku Yi Yajin Aiki, Mu Kore Ku A Aiki –Gwamnatin Kaduna

Daga Abdullahi Usman, Kaduna

Kungiyar Malaman Makarantun Firamare reshen Jihar Kaduna ta bayyana aniyarta na shiga yajin aikin bai daya yau litinin don nuna adawarta da shirin gwamnatin jihar Kaduna na korar Malaman jihar dubu ashirin da biyu da gwamnatin jihar ta yi a kwanan baya.

A takardar da kungiyar ta raba wa manema labarai, wanda sakatarenta Kwamared Ango ya sanyawa hannu, ta nemi Malaman makarantun firamare da sakandare na gwamnati da su tsunduma a wannan yajin aikin.

Ta kuma bayyana cewa sun yi bakin kokarinsu don ganin sasanta da Gwamnatin jihar cikin ruwan sanyi amma abin ya gagara. Suka ce sun tafi kotu, in da ta baiwa gwamnatin jihar umarnin ta ta dakatar da shirinta na sallamar Malamai dubu ashirin da biyu da Gwamnatin jihar ta yi, amma Gwamnatin ta yi biris da wannan umarni na kotu. In da ta ba da umarnin da a rabawa Malaman da ta sallama takardar kora. Don haka suka ce ba su da wani abu da ya rage musu face su ci gaba da bin hanyoyin da suka halasta don neman hakkinsu. Don haka suka bayyana cewa daga gobe za su fara wannan yajin aikin.

Sai dai kuma Gwamnatin jihar ba ta ji dadin wannan matsaya da kungiyar ta dauka ba. A ta bakin Gwamnatin jihar Kaduna, ta bayyana cewa duk Malamin da ya ki zuwa wurin aiki a yau, to ya tabbatar da cewa Gwamnatin jihar ta koreshi daga aikinsa. In ji Gwamnatin a sanarwar da babban mai magana da yawun Gwamnan Mista Samuel Aruwan ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa Gwamnati ta sami labarin cewa kungiyar Malaman Makarantun firamare reshen jihar na shirin shiga yajin aikin sai mama ta gani yau, ba za ta zura ido ba ta ga wasu suna yadda suka ga dama ba da sunan yajin aiki haramtacce. Ta ce hakan kokari ne na lalata ilimi a jihar.

Jihar Kaduna ba ta da lpkacin biyewa kungiyar saboda Gwamnati ta sallami Malaman da ba su iya aikinsu ba. Sabo da haka rayuwar daliban jihar Kaduna miliyan biyu ya fi muhimmanci a kan ci gaba da barin Malaman da ba su da kwarewa.

Gwamnatin ta ci gaba da cewa, gwamnatin tarayya ta shiga tsakani in da ta kira taro a Abuja, Gwamnan jihar Kaduna nan ne ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar a daya daga cikin zaman in da kuma ya bayyana musu cewa gwamnati ce ta dauki ma’aikatanta kuma tana da ikon sallamarsu.

Sanarawar ta ci gaba da cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta umarci dukkan makarantun jihar da su bude rajistar ma’aikata a yau litinin, duk Malamin da ya ki zuwa aiki za a hukuntashi da dokokin da suka tanadi hukunta wanda ya ki zuwa aiki.

Daga nan sanarwar ta gargadi shugabannin kungiyar Malaman kan cewa ta guji zuga Malaman jihar. Ta ce dama kwanan baya kungiyar ta yi yunkurin sanya Malaman yin zanga-zanga in da har suka bata kayan gwamnati a majalisar dokokin jihar Kaduna. Don haka Gwamnatin ta jaddada aniyarta na hukunta shugabannin kungiyar kan yin zanga-zanga ba tare da izini ba.

Exit mobile version