CRI Hausa" />

Ana Yaki Da Cutar COVID-19 A Jihar Xinjiang Bisa Ka’idojin Sanya Jama’a Da Rayuwarsu A Gaban Kome

Direktan kwamitin kiwon lafiya na jihar Xinjiang ta kasar Sin, Mutharifu Rozi ya bayyana a kwanakin baya cewa, bayan samun barkewar cutar COVID-19 a yankin Kashgar dake jihar, an bi ka’idojin sanya jama’a da rayuwarsu a gaban kome, da kara yin imani da hadin gwiwa tare don yaki da cutar da daukar matakai bisa yanayin da ake ciki, ana kuma kokarin daukar matakai masu dacewa don hana yaduwar cutar da kuma tabbatar da lafiyar jama’ar kabilu daban daban dake jihar.

Bayan barkewar cutar a jihar, an tura rukunonin ma’aikata da masana zuwa yankin Kashgar ba tare da bata lokaci ba don jagorantar yaki da cutar, da samar da shirin ko ta kwana, da gano asalin yaduwarta da yanke hanyoyin yaduwar. Kana an yi bincike kan dukkan mutanen dake yankin, da bada jinya yadda ya kamata, da soke kudin jinyar bisa manufofin da aka tsara, da tabbatar da samar da kayayyaki da zaunar da farashinsu, da kuma daukar matakan magance yaduwar cutar a yau da kullum. (Zainab)

Exit mobile version