Ana Zargin Direba Da Kashe Ubangidansa Tare Da Jefa Gawar A Masai

An kama wani direba mai suna Samson, a bisa tuhumar da ake yi masa na kashe Ubangidansa da kuma jefa gawar a cikin Masai. Ana zargin aikata laifin kisan ne a Anguwar Ekiadokor da ke Karamar Hukumar Obia ta Arewa maso Gabas, da ke Jihar Edo. Hakanan sauran mutane biyun da ake zargi a kan aikata laifin na kisa, su ma sun shiga hannu.

An bayar da labarin cewa, Samson din ya sayar da motar Ubangidan na shi ne ga wani Boka da ke zaune a kauyen Oybiogie, inda kuma ya dawo ya shaidawa ‘Ya’yan mamacin cewa an yi garkuwa da Uban na su.

Majiyar ‘Yan Sanda ta ce, Samson din ya shaidawa ‘Ya’yan mamacin wadanda suke zaune a wajen kasarnan cewa, Masu garkuwa da mutanan da suka kama Uban na su sun nemi da a biya su kudaden fansa har Naira Milyan Biyu. “Samson ya karbi wasu kudi daga ‘Ya’yan Ubangidan na shi, a bisa alkawarin da ya yi masu na cewa ba da jimawa ba za a sako Uban na su,” in ji majiyar.

Likin ya tashi ne a sa’ilin da wasu ‘yan’uwan mamacin suka ziyarci gidan mamacin, kuma suka gano gawar na shi da har ta fara kmbura a cikin Masan gidan. ‘Yan Sanda ne daga Ofishin ‘Yan Sanda na Ekiadolor, suka kama direban a lokacin da yake kokarin karbar sauran cikon kudi Naira 500,000, na motar mamacin da ya sayar wa Bokan.

A wani labarin kuma mai kama da wannan, ‘Yan Sanda sun kama wata Mata mai shayarwa mai suna Janet Usen, da kuma wasu mutane uku, a bisa tuhumarsu da laifin sace wani karamin yaro mai shekaru 4, mai suna Gideon da ke zaune a kan titin Atamunu na garin Kalaba, cibiyar Jihar Kros Riba. A yanzun haka kuma wadanda ake zargi da aikata laifin suna garkame ne a Ofishin ‘Yan Sanda na kan titin saukan Jiragen sama, Atimbo.

An sami labarin cewa sun sace yaron ne, inda suka boye shi a wani gida da ke can Anguwar ta Atimbo din. wani makwabcin gidan ne ya lura da cewa, yana ganin yara bakin fuskoki daban-daban ana kawo su cikin gidan, inda nan take ya radawa masu unguwannin wajen. Inda masu anguwannin suka tunkari masu laifin, nan take kuma ba su baiwa shari’a wahala ba, inda suka tabbatar masu da cewa, lallai sato yaron suka yi. A nan ne aka kira ‘Yan Sanda domin su shiga Tsakani.

Kakakin rundunar ta ‘Yan Sanda na Jihar, ASP Irene Ugbo, ya tabbatar da cewa, tabbas sun kama mutanan hudu da ake zargi, kuma suna nan suna ci gaba da binciken gaskiyan abin da ya faru.

 

 

Exit mobile version