Mahukunta a Spaniya suna zargin ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid Marcelo da ƙin biyan haraji da ya kai kudi fam dubu dubu dari hudu da talatin da shida..
Masu shigar da kara sun alakanta rashin bin ka’ida da ɗ an ƙwallon ya yi ta hanyar bude kamfani a waje da yake kula da kudin da yake samu ta fuskar tallace-tallace.
Har yanzu dai Marcelo mai shekara 29 ɗ an ƙwallon tawagar Brazil, bai ce komai ba ɗ angane da zargin da ake masa.
Shi ne ɗ an wasa na baya-bayan nan da mahukuntan Spaniya ke zargi da kaucewa biyan haraji, bayan Messi da Neymar da Ronaldo.
Masu sharhi akan wasanni dai suna ganin wataƙila akwai matsala a cikin hukumar kula da haraji ta ƙasar ta sifen saboda ana yawan samun irin wannan matsalar.
A kwanakin baya Cristiano Ronaldo yayi barazanar barin real Madrid bayan zargin da akayi masa inda ya bayyana cewa baya samun goyon baya daga real Madrid.