Anas Haqqani: Sojojin Amurka Su Ne Ainihin Wadanda Ke Barna A Kasar Afghanistan

Daga CRI Hausa,

Wakilinmu da ke birnin Kabul ya samu damar tattaunawa da babban jagoran kungiyar Taliban Anas Haqqani, wanda da ya yi bayani kan hare-haren da sojojin Amurka suka kaddamar kafin su janye daga kasar wadanda suka haddasa mummunan hasarar rayukan fararen hula da jikkatarsu, ya ce, a cikin shekaru 20 da suka wuce, sojojin Amurka sun sha bayyana kungiyar Taliban a matsayin wadanda ke halaka fararen hular Afghanistan, amma a hakika sojojin Amurka su ne ainihin wadanda ke yin barna a kasar.

Anas Haqqani ya kara da cewa, bayan da ‘yan kungiyar Taliban suka shiga birnin Kabul, ba su lalata kome ba, kuma suna fatan ba za a lalata filin jirgin sama ba, wanda ya kasance alamar ikon kasar, kuma jiragen sama ma kadarorin kasar ne, amma abin bakin ciki shi ne, sojojin Amurka sun lalata jiragen sama da ma sauran na’urori da dama kafin janyewarsu.(Lubabatu)

Exit mobile version