Umar Faruk" />

Anchor Borrowers: Shinkafa Ton Miliyan 3.5 Manoma Su Ka Samar A Kebbi

Kungiyar noman shinkafa ta kasa reshin jihar Kebbi (RIFAN), ta bayyana cewar, manoman shinkafa a jihar Kebbi sun samar da shinkafa ton miliyan 3.5 a noman rani na bana a jihar.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar na jihar, Alhaji Muhammad Sahabi Augie, yayin wani taron tattaunawa da suka gudanar tare da manema labaru a Birnin-Kebbi a jiya.

Ya ce, ”manoman sun noma shinkafa ton miliyan 1.5 a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin anchor Borrowers a 17 ga watan Nuwamba na shekara ta 2015. “ A shekarar farko na shirin noman shinkafar rani, an samu shinkafa ton 700,000 , haka kuma an samar da ton miliyan 1.5 , wanda a shekarar farko ne aka samar da wadannan , amma daga nan manoman shinkafar a jihar ta Kebbi sun kara bisa ga abin da aka samu a shekarar farko na shirin.

Haka kuma ya cigaba da cewar “a wannan shekara manoman shinkafa sun samar da shinkafa ton miliyan 3.5 wanda yawuce kashi 150 na abinda aka samar a nomaman shinka na bana. Bugu da kari shugaban kungiyar yace” bisa ga cigaban da aka samu kan irin mizamin yawan nauyin shinkafar da a ke samar wa a Jihar Kebbi a shekara ta 2016, ya san wasu kasashe suka shigo jihar don sayen shinkafar da manonma su ka noma, kasashen sun hada da Mali, Kamaru, jamhuriyar Nijar da kuma ta Benin da sauran wasu kasashe, saboda ganin irin yadda manoma jihar Kebbi ke samar da miliyoyin ton din shinkafa ta hanyar noman rani,” in ji shi.

Har ila yau ya ce, “kamfunan casar shinkafa a jihar ta Kebbi da ma wasu jahohin kasar nan su kan samu shinkafar su ne daga manoman jihar ne, batare da sun tafi wani wuri ko wata jaha ko kuma wasa kasa kafin samun shinkafar da zasu cashe ba. Hakazalika ya kara da cewar”babu yadda za’ayi wani ya iya karkata akalar wannan tsarin bada tallafin noma a jihar ta Kebbi ga manoma domin yana da nashi tsare kafin karbar tallafin noma, bugu da kari bankin bada tallafin bashin noma ga manoma shi ne ya bada wannan tallafin ga dukkan manoman jihar ta Kebbi wato bankin BOA da a ke kira a turance ‘Bank of Agriclture’ da ke a Birnin-Kebbi.

Har ila yau ya ce” muna da hujjo da kuma takardun sheda na tabbar da cewar manoma na gaskiya ke akwai a jihar Kebbi”, inji shugaban kungiyar Shabi Augie. Ya kuma ce, “matsalar da kungiyar ta samu shine wurin karbar bashin da aka baiwa manoma a jihar wanda har yanzu muna kokarin ganin cewar mun karbo sauran bashin tallafin da bankin bada bashin manoma ya baiwa manomanmu.”

A cewar shugaban kungiyar manoman shinkafa, a cikin manoma 700,000 da su ka ci gajiyar tallafin, manoma dari biyu ne kawai su ka kammala biyan bashin tallafin da su ka karba.

jihar ta K˙ebbi sun karbi tallafin kudi da kayan noman rani na Naira Biliyan 12.8 ta hannun Bankin bada bashin noma ga manoman shinkafa a jihar ta Kebbi.

Ya cigaba da cewar, “duk manomin da ya cigajiyar bashin sai da aka umurce shi da bude asusun ajiya(Bank account ) wanda ta wannan asusun ne manomi zai karbi kudin tallafin. Haka kuma tallafin ya kunshi kudi da kayan noma da aka bawai duk manomi a jiha, a cewarsa.

Udulu ya kara da cewar, “ba dukkan manoma saka karbi cikakin kudi ba, saboda an bada su ne bisa ga mataki-mataki kan iya wurin manomi iya kudin sa.

Da ya ke jawabi tun farko, manajan bankin bada bashin manoma na jihar ta Kebbi, Alhaji Aliyu Zurmi, ya tabbartar da bayyanan da mambobbin Anchor Borrowers na jihar suka gabatar wa manema labaru a Birnin-Kebbi a jiya cewa” an bawai manoman jihar Kebbi tallafin kudin noma ne ta hannun bankin bada bashin noma da ke Birnin-Kebbi .

Bugu da kari ya ce, “gwamnatin jihar Kebbi ta cikin bada tallafi ga manoma ko hannu ga rabon kudin tallafin noma na jihar, wanda bankin bada bashin manoma ne ya bawai manoma jihar bashin noma, amma kuma sai banki ya tantance manomi kafin bashi tallafin . Kazalika Zurmi ya cewa “manoma na kananan hukumomi 21 ne a jihar suka amfana da wannan tallafi na bankin bada bashin manoma a jihar ta Kebbi.

Daga nan ya ce “ba tallafin gwamnatin jihar Kebbi ba ne , wannan kudi bankin bada bashin manoma ne kuma bankin ne ya bada bashin da kansa , gwamnatin jihar Kebbi ta tsayawa manoman jihar ne kawai”, inji zurmi. Saboda hakan muna kira ga dukkan manoman da suka ci gajiyar tallafin noma su tabbatar da suka kammala biyan bashin da suka karba na tallafin noma a bankin.

Exit mobile version