Abba Ibrahim Wada" />

Andersen Yana Son Komawa Arsenal

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Sampdoria, Joacham Andersen ya bayyana cewa babban burinsa shine yaga yana bugawa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal wasa a kakar wasa mai zuwa idan an fara.

Tauraruwar dan wasa Joachim Andersen ta haska dai musamman a kakar wasan data gabata inda ya buga wasanni 32 a kungiyar wanda hakan yasa kungiyoyi da dama ciki har da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham suka shiga zawarcin dan wasan.

Dan wasan dan asalin kasar Denmark ya bayyana cewa yana son barin kungiyar tasa kuma gasar firimiya yake son komawa hakan yasa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta fara fatan ganin ta kulla yarjejeniya da dan wasan kafin ta fara ciniki da kungiyar tasa.

“Lokaci yayi da zan matsa daga inda nake domin neman karin kwarewa da kuma sanin abubuwa da daman a rayuwa amma kuma har yanzu ina son kungiya ta ta Sampdoria sai dai ina fatan idan nasamu dama zan bar kungiyar” in ji Andersen

Ya cigaba da cewa “Akwai kungiyoyi masu kyau a nahiyar turai da suke Magana da wakilina kuma ina fatan zan zauna dani da iyalina domin neman mafita wato kungiyar da yakamata in koma a kakar wasa mai zuwa’

A karshe yace yana da burin bugawa manyan kungiyoyin duniya wasa saboda haka yana fatan wannan ne lokacin da zai fara ganin mafarkinsa ya fara zama gaskiya sai dai kungiyar kwallon kafa ta AC Milan ma tana daya daga cikin kungiyoyin da suke zawarcin dan wasan.

Exit mobile version