Abdullahi Muhammad Sheka" />

Ango Ya Kashe Amaryarsa Bayan Wata Daya Da Aure

Wani Ango mai shekara 26 da haihuwa, mai Suna Aminu Inuwa  da ke zaune a Unguwar Jakada a Birnin Kano, ya kashe Amaryarsa mai Suna Safara’u har lahira tare da bizne ta a cikin gidansu da suka tare. Wani makwabcin gidan ne ya tsegunta wa dattijan unguwar cewar wanda ake zargin ya tuntube shi  da wasu jerin tambayoyi ciki har da yadda ake bizne gawar mamaci tare kuma da neman sanin hukuncin da addinin Musulunci ya tanada kan duk wanda ya kashe mutum.

Ya ci gaba da cewa ya yin da ya shiga cikin gidan makwabcin da ake zargi, ya iske jini ko ina a cikin gidan sannan kuma ya ga wani wuri da aka haka wanda ya yi kama da Kabari.

Wanda ake zargi Aminu Inuwa ya bayayanawa manema labarai cewar ya kashe matarsa ne sakamakon rashin yi masa biyayya.  Ya ce babu shakka “ina mutukar son ta a matsayin matata, kamar yadda ita ma ta ke mutukar sona, ta yadda har ba na zaton iya rayuwa ba tare da ita ba. Abin da ya faru tsautsayi ne kawai ba da gangan ba ne,” in ji Aminu Inuwa.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna ya tabbatar da wannan labari inda ya ce yanzu haka wanda ake zargin na hannun jami’an tsaro. Ya ce wani mutun mai shekara 26 dake zaune a unguwar Jakada a Jihar Kano ya yanka matarsa  mai shekara 18 da haihuwa mai suna  Safara’u, wanda ya tona kabari a cikin gidansa ya bizne ta.

Tuni Jami’an tsaron suka tone Kabarin tare da dauke gawar zuwa asibitin kwararru na Murtala domin adanawa.

Yanzu haka wanda ake zargin na hannun jami’an ‘yan sanda kuma tuni aka kaddamar da bincike. Da zarar an kammala bincike za a gabatar da shi gaban kotun da ta ke da hurumin sauraran karar domin girbar abin da ya shuka, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ya bayyana.

A cewar makwabcin wanda ake zargi da kisan, Aminu Inuwa ya auro Safara’u ne daga garin Azare a Jihar Bauchi wata guda da ya gabata.

Exit mobile version