Ango Ya Nemi Rabuwa Da Amaryarsa Saboda Yawan Fitsarin Kwance

Wani sabon ango ya bukaci kotu ta raba auren sa da amaryarsa saboda fitsarin kwance da ta ke yi a kowani dare.

Angon mai suna Mista Deji, ya bayyana hakan a Ibadan ta jihar Oyo, ya ce amaryarsa da ba su dade da yin aure ba tun tarewarta ta ke yin fitsarin kwance wanda rabuwarsu ya zama dole domin ya sabawa al’adar inda ya fito.

Mista Deji ya bayyana hakan ne a wata ‘yar wasikar da ya rubutawa makusantar amaryar tasa, inda ya yi korafi akan fitsarin kwance da amaryar ke yi a kowani dare, inda ya ce akan wannan matsalar ma ya bar gidansa.

Mista Deji, ya cigaba cewar gaskiya ina cikin matsala akan wannan lamari, na fitsarin amaryata auren da bai wuce wata uku da yin sa ba, ya ce na auri yarinya ‘yar Benin da ake cewa Adesuwa, ba mu taba hada tabarma da ita ba har muka yi aure saboda wannan halin na aure ta ban san tana da mugun hali ba.

Ina zargin ta san da wannan matsalar tsawon lokaci, ta yaudare ni alhalin tana da shekaru ashirin da tara a duniya.

A bangaren Ibadan da na fito tsarin kwance al’adar mu bai amince da shi ba. Na yiwa baba korafi akan wannan matsalar ya ce a tsohuwar al’adarmu a na neman maganin sa dan haka bai ga wata damuwa akan wannan matsalar ba in har tana da hali mai kyau. Mahaifiyata ma matsayin ta daya da baba na da wasu ‘yan uwana da na tattauna da su.

Gaskiya mata ta, tana daga cikin matan da suka da ce a matsayinta na ma’aikaciyar jinya, tana kwazo da jajircewa.

Tun lokacin da na yi auren nan kusan dukkanin abokan ciniki na da na ke anfana su cinikin ya koma ba shi. Tun lokacin da na fahimci hakan na kauracewa gida na, na koma gidan abokina.

Saboda ganin hakan matar abokin na wa ta kora ni dan in koma in shirya da mata ta, ta ba ni kwana biyu in bar masu gidan su.

Na gaya mata ta bar min gida kafin in dawo daga inda na ke gudun hijira a cikin satin nan.

Gaskiya yanzu ba na cikin hayacina, saboda na bar budurwata bayarba na auri ‘yar Benin, kuma ga halin da na ke ciki da ita, kuma ban da damar rabuwa da ita saboda wai lokacin zaman mu yayi kusa da a ce mun rabu domin kotu ma ba za ta amince  da raba auren mu ba.

Exit mobile version