Mahdi Garba" />

Annobar Kodin: Ina Gizon Yake Saka?

Babu makawa duk wanda ya san kodin zai gane cewa annobar kullum kara ta’azzara take kamar wutar daji. Matsalar ta wuce yadda Gwamnati take tunani.

Biyo bayan haramta kodin din da Gwamnatin tarayya tayi ranar 1 ga watan Mayu hakan ya kara fitowa fili. Bai kamata Gwamnati ta dogara da rahoton da BBC Africa ta yi ba.

Kafin haramta wannan abu mai mugun hatsari ya kamata Gwamnati ta kaddamar da kwamitin bincike ne don binciko dalilin da ya sa annobar take kara ta’azzara, dalilin da ma ya sa tun farko suke bigewa da wannan dabi’ar, kai har masu cin moriyar kazamar harkar.

Sanin kowa ne haramta abu a Gwamnatance bai taba zama mafita kuma ba zai zama ba. Tunda an dade da haramta wiwi da kokino amma an daina sha?

Sannan haramta kodin din da Gwamnatin tarayya tayi sai yayi kamar ba ta gane ma inda gizon yake balle a dau matakin da ya dace.

Bayan kodin akwai miyagun kwayoyin da ake sayar dasu yanzu  tamkar gyada musamman a jihohin Kano, Kaduna, Filato, Katsina, Gombe Yobe, Bauchi, Borno da sauran jihohin Arewa.

Abin da ya cika jaridu da shafukkan sada zumunta akan shaye-shayen nan shine wai mafi yawan ‘Yan kodin din matasa ne da matan aure. Lallai duk mai fadin haka ya raina irin karbuwar kodin tayi a Kasar nan.

A bangaren matasa daga kan daliban firamare, zuwa na Sakandire har zuwa na jami’a babu wanda annobar ta kyale. A janibin iyaye kuwa babu mazan balle matan.  Idan aka dawo gefen masu ruwa-da-tsaki anan ne zaka ji sunayen da ko a mafarki baka tunanin jin su.

A wani binciken diddigi da jaridar Daily Trust tayi  a ranar 29 ga watan Disamban shekarar 2012, ta ruwaito wata ‘Yar kodin a jihar Gombe tana fadawa wakilin jaridar har ‘Yan Majalisa na shan sinadarin kodin din. Tace mashayin yana zabin sha kai tsaye ko kuma ya hada da Coca-Cola.

Idan kuwa haka ne kun ga masu dora alhakin shan kodin akan samari da ‘yan mata na da karancin sani akan barnar wannan annobar.

Na Matasan dai ya fito fili ne saboda soyayyarsu da  hamshakan ‘Yan kodin din duniya masu fakewa da wakoki suna gurbata tarbiyyar matasa irinsu Lil Wayne, Wiz Khalifa da Tyga. Babu makawa irin wakokin bidiyon mawakan ya taimaka sosai wajen gurbata tarbiyar matasan nan.

Irin abubuwan da Gwamnati ta manta dasu kenan. Mafi yawan wadanda suka fada tarkon shan miyagun kwayoyin nan idan zaka saurari yadda suka fara harkar dole kaji an kira abokai a unguwa ko makaranta, ko kuma damuwan talauci da yanayin rayuwa ko rashin jin dadin zaman aure (a wajen mata kenan) sai kuma popular culture ko yayi.

A lokacin da suka shiga harkar babu wani tunanin abin da zai je ya dawo kamar hadurran dake tare da shaye-shayen. Wanda idan da Malaman addini, iyaye, ‘yan jaridu, marubuta da masu ruwa-da-tsaki suna fadakarwa akan hakan da barnar bata kai haka ba.

Hadurran kodin sun wuce duk yadda alkaluma suke misaltawa.

Bayan dauke da sinadarin nicotine wanda yake kai mutum ga masifar son abin, akwai wasu da dama. Amma saboda son abin da nicotine yake shigarwa da mutum daga nan sai ya zama addicted. Ko kudin waye a hannunshi zai je ya sayo ya sha. Ko kudin makaranta ne, ko wani abu da zai sayar ya samu kudi irinsu wayoyin hannu, kwamfutoci da kuma kayan sawa idan tsiyar ta kai makura. Kai! Anan kuma idan ya gama sayar da abubuwanshi sai a shiga sace-sace.

Za su iya baka wayar sata ta dubu ashirin akan kodin kwalba biyu abin da bai fi Naira 2,000 ba. Shi ya sace-sace da kwace yayi yawa acikin al’umma.

A binciken da nayi sai na karo gano kodin yana daga cikin magungunan da ake kiransu aphrodisiac, wato magunguna masu ta da sha’awar namiji ko mace. Shiyasa matsalar fyade da zinace-zinace suke ci gaba da karuwa acikin al’umma.

Wannan illolin da kodin ya ke dashi dashi kenan acikin al’umma.

Sai kuma ga lafiyar su masu shan wadannan abubuwan. Masana kiwon lafiya sun ce kodin yana haifar da cututtuka da dama, amma ciwon hanta da ciwon koda sune fitattatu da aka sani.

Abin lura dai shine; akasarin abubuwan ashsha dake faruwa yanzu za a iya jinginasu ga shaye-shayen kodin wanda har matan da ake kira matan-kulle suna sha.

Yanzu dai ya ragewa Gwamnati da Iyayen yara sun san hanyar da za su bi domin dakile wannan annobar da kullum kara ci take kama wutar daji.

Wajibi ne iyaye su kara sa ido akan  ‘ya’yansu da abokan huldarsu a gida da makaranta. Dole kuma su kara lura da ‘ya’yansu lokutan bukukuwan aure musamman na Sallah. Yara da dama sun fada hatsarin da babu yadda aka iya dasu a lokutan yawon sallah.

Idan kuma Gwamnatin tarayyar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake jagoranta da ma’aikatar kiwon lafiya ta Kasa karkashin jagorancin Farfesa Isaac Adewale sun shirya magance wannan matsalar dole su tsaya suyi abin da ya dace ta hanyar binciken musabbabin matsalar tunda a da can babu ita.

Wajibi ne Gwamnati tayi kokarin samarwa ‘Yan Kasa aikin yi, don zaman kashe-wando babu abin da ba zai sa ba.

Ya zama tilas wa Gwamnati ta bullo da hanyar fadakarwa akan hadurran dake tattare da shan kodin.

Kuma ya kamata Gwamnati ta bude gidajen ladabtar da mutane ‘rehabilitation centers’ a kananan hukumomi 774 dake tarayyar Nijeriya saboda nutsar da wadanda suke da niyyar tuba.

Haka kuma, majalisar dokoki dole tayi dokar kare hakkinsu da mutuncinsu domin rashin yin hakan zai kara nisantar dasu daga cikin al’umma ko bayan sun tuba.

Sannan a kara sa ido ga irin magungunan da ake hadawa a kasar da kuma shigowa dasu. Idan hukumar NAFDAC tayi aiki kamar yadda aka kirkireta dole a samu sauki.

Daga karshe kuma dole Gwamnati ta san suwa take baiwa a aiki a hukumar NDLEA. Sannan a samar da tsarin shirya musu tarukkan bita akai -akai don gane sabbin salon tunkurar masu cin moriyar wannan tabargazar.

Mahdi ya rubuto daga Jos.  Ana iya samunsa a:

Imel: Mahdigarba@gmail.com

Tiwita: @MahdiGarba

 

Exit mobile version