Daga Zubairu M.Lawal, Lafia
Daraktan tabbatar da ingancin ilimi na Jahar Lagos, Misis Abiola Seriki Ayeni, ta bayyana cewa, annobar Korona ba za ta iya hana dalibai zuwa makaranta bakidaya ba.
Ta bayyana hakan ne a wajen taron duba matsalolin ilimi, wanda Hukumar Majalisar dinkin Duniya ta UNESCO ta shirya a Abuja.
Abiola Seriki Ayeni ta ce yadda cutar korona bairos ya janyo illa a fannin ilimi wanda ya kamata a tattauna akai da kuma yadda za’a shawo kanshi ta hanyar ganin an habbaka ilimi, an farfado dashi da kuma ganin an koma makarantu baki daya ba tare da rarrabawa wani jihar suna karatu wasu jihar suna zaman gida ba.
Ta kara da cewa zaman yara a gidajen su babu abinda zai amfanar face kara fadawa matsalar rashin ingantaciyar ilumi.
Tace ya makata Gwamnatoci su dauki matakin yaki da yaduwar cutar ta ko ina a cikin kasa. Hakama makarantu su dauki matakin ta hanyar kulawa da yara a kula da zurga zurgansu da tsaftace hannaye da sauransu.
Shima a nasa jawabin Mista Mamadou Lamine Sow ya ce Illar da annobar korona yayiwa harkar ilimi a Duniya abu ne wanda ya kamata ayi magana a kanshi dan ganin an habbaka harkar ilimi da kuma gudun ilimi ya dinga fadawa cikin wani yanayi na rikici da kuma koma baya.
Mista Mamadou Lamine Sow, shine babban mai lura da ilimi a karkashin kungiyar UNESCO shiyyar ABUJA dake tarayyar Nijeriya.
Mista Mamadou Lamine Sow, yayi bayani mai kayatarwa a wajen taron da ya gudanar ta yanar gizo wanda kungiyar UNESCO ta shirya, a Sashin tabbatar da ingancin ilimi na jahar Lagos da kuma kungiyar nan mai bada agaji mai suna (Nurturage charity foundation), don tunawa da mahimmancin Ilimi a duniya.
Ya ce ya zama wajibi Gwamnati da kuma masu fada aji su kawo tsari da hanyoyin da za’abi dan ganin ba’a bar dalibai sun cigaba da zama ba tare da cigaba da kataru ba, a lokacin da korona bairos takawo nakasu a harkar ilimi
Mista lamine-Sow yayi kira ga masu fada aji hadda gwamnati su hada hannu da karfe wajen ganin an rage cin koson dalibai masu karatu a cikin ajujuwa.
Daraktan tabbatar da ingancin ilimi na jahar Lagos Misis Abiola Seriki Ayeni tayi bayani kan yadda cutar korona bairos ya janyo illa a fannin ilimi wanda ya kamata a tattauna akai da kuma yadda za’a shawo kanshi ta hanyar ganin an habbaka ilimi, an farfado dashi da kuma ganin an koma makarantu baki daya.
Ta kara da cewa zaman yara a gidajen su babu abinda zai amfanar face kara fadawa matsalar rashin ingantaciyar ilumi.
Tace ya makata Gwamnatoci su dauki matakin yaki da yaduwar cutar ta ko ina a cikin kasa. Hakama makarantu su dauki matakin ta hanyar kulawa da yara a kula da zurga zurgansu da tsaftace hannaye da sauransu.