Connect with us

LABARAI

Annobar Korona: Buhari Da Trump Sun Yi Wa Juna Jaje

Published

on

A yinin ranar Talata ne, Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya amsa waya daga Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump, inda shugabannin biyu su ka taya junansu jimamin rashe-rashen da kasashen nasu su ka yi a sakamakon barkewar annobar Korana.

Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Mista Femi Adesina, wanda ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya ce, shugabannin biyu sun kuma yi musayar ra’ayi a tsakaninsu kan hanyoyin da ya kamata a bi wajen shawo kan annobar ta Korona cikin gaggawa.

Adesina ya ruwaito shugaban nasa ya na bayyana ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar kasar ta Amurka a bisa dimbin rashe-rashen da kasar ta yi a sakamakon barkewar annobar ta Korona a can da kuma yadda ta ta’azzara, sannan ya nuna damuwarsa a kan yawan mutanen da su ka mutu sakamakon barkewar annobar a ma fadin duka duniyar nan.

“Shugabannin biyu sun kuma tattauna a kan barnar da annobar ta haifar wa tattalin arzikin duniya. Shugaba Buhari ya kuma yaba wa takwaran nashi na Amurka matakan da ya dauka, domin dakile yaduwar annobar a sassan kasar ta Amurka,” kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasar ya bayyana.

A cewar Adesina, Shugaba Buhari ya nuna aniyar Nijeriya na hada kai da kasar Amurka wajen yakar babban makiyar tasu da ba a ganin ta a bayyane, wato Annobar Korona.

“Shugaba Buhari ya sanarwa da takwaran nashi na Amurka irin matakan da kasar nan ta dauka, domin dakile yaduwar annobar Korona a duk sassan kasar nan.

“Shugaban kuma ya yi murna da irin dangartakar da ke tsakanin kasashen biyu, sannan ya yi godiya ga Shugaba Trump a kan kiran wayar da ya yi ma sa a irin wannan mawuyacin yanayin,” in ji sanarwar fadar shugaban.
Advertisement

labarai