Wata tsutsa mai lalata amfanin gona ta bayyana a wasu yankunan ƙasar Chadi, inda tuni ta fara yin mummunan ta’addi ga amfanin gona, almarin da ke matuƙar barazana ga wadatuwar abinci a ƙasar.
Tsutsar wadda asalinta aka ce ta fara ne a ƙasar Amurka, a cikin wannan shekara ta lalata ɗimbin amfanin gona a ƙasashen kudancin Afirka, kafin daga bisani ta isa ƙasar ta Chadi.
Malam Sanusi, wani manomi a ƙauyen Yarwa Baktaba, ya ce Tsutsar tun tana ƙarama ta ke ta’adi har ta girma, kuma duk amfanin gonar da ta ci karo da shi ta ke cinyewa.
Sannan Tsutsar ta bambanta akwai mai cin amfanin gona idan ya fito, kamar gero da dawa da ta ke ci daga ciki ta mayar gari akwai kuma ta ƙasa da ke lalata shuka a cewar Malam Sanusi.
A watan Afrilu ne Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tsutsar wacce ke cinye amfanin gona ta isa ƙasashen Rwanda da Kenya, bayan ta’adin da ta yi a wasu ƙasashen da ke kudancin Afirka.