Annobar Zazzabin Lassa Likitoci Sun Ja Hankalin Al’ummar Inugu

A jihar Inugu  gwamnatin jihar na kokarin ta yi maganin annobar zazzabin Lassa,musamman ma da take kusa da jihar Ebonyi, wurin da aka ce ma’aikatan lafiya 40 sun mutu, saboda ita babbar annobar data addabi jihar.

Babban jami’in lafiya matakin farko na ma’aikatar lafiya ta jihar Inugu Dokta Okechukwu Ossai ya ja hankalin mutane, da su guji kone daji, domin a guje ma yadda su berayen zasu shiga cikin  .

Dokta Ossai ya bada shawarar ne wajen ganawa da ya yi da manema labarai a Inugu cewar, idan aka bar kone daji, zai rage yawan shigar da beraye suke zuwa gidajen mutane, ta hakan a cewar shi za ayi maganin bazuwar ita cutar, wadda ake kamuwa da ita saboda bera wanda ke dauke da cutar.

Ya cigaba da cewar ‘’ Gwamnatin jiha ta fitar da doka wadda ke nuna duk wanda aka kama yana kona daji, za ayi ma shi duk hukunci da aka ga dama. Kone daji yana kawo kwayoyin cuta, bayan nan kuma berayen dake dajin zasu shiga gidajen mutane’’.

‘’Duk lokacin da muka kona dazuzzukan da suke kusa damu beraye suna rugawa su shige gidajen mu, daganan zasu bata abincinmu idan suka ci, da kuma yin fitsari da kashin su, wannan kuma shi ne ke sa  a kamu da cutar Lasa.’’

Ya ba mutane shawarar da su lura da tsaftace muhallinsu da su kansu, ya kuma kara da cewar yana da matukar muhimmanci a rika rufe duk kayayyakin abinci, saboda yin hakan zai sa  samu raguwar yaduwar ita cutar.

‘Ya kamata mutane su lura sosai, su kum kiyayi duk wata hukda da wanda ya kamu da cutar, duk wanda ya fara jin alamar shi zazzabin, ayi maza a je asbitin da ke kusa domin a samu taimako, wanda zai taimaka kada abin ya ricabe’.

Wata Kungiya Ta Yi Kira Da Gwamnati Ta Kawo Karshen Bambanci Tsakanin Digiri Da HND

Daga Idris Aliyu Daudawa

Wata kumgiya a karkashin The Coalation of Concerned HND holders a Nijeriya ra yi kira da gwamnatin tarayya, da ta kawo karshen wani mataki da aka dauka, wajen kammala shi gaba daya, wanda ya kawo karshen bambancin da ake akwai wurin aiki tsakanin mai takardar sjaidar ilmi ta HND da kuma Digiri. Shi dai an cimma daukar wannan mataki ne a shekarar 2016.

Ita wannan kungiya ta yi kira da shugaban ma’aikata na kasa cewar a aika shi wannan kudurin zuwa majalisar zartarwa ta kasa, domin ta bada dama a fara mafani da sabon tsarin na daidaituwa.

Kungiyar a wata takarda mai dauke da kwanan sa  watan Janairu 18 wadda kuma aka yi  ma adireshinta, zuwa ofishin shugabar ma’aikata mai suna Mrs Winigfred Oyo- Ita, kungiyar ta ce, a tuna fa akwai wani kuduri wanda aka cimmawa ranar 22 ga watan Yuli na shekarar 2016. Taro ne na National Council om Establishment, cewar a kawo karshen bambancin da ke akwai wanda aka dade ana yi,dangane da Satifiket na digiri da kuam babbar difiloma ta kasa, sun kuma nemi da ayi amfani da matakai ukun da ake dauka aka kuma amince da su lokacin taron.

Takardai ta ci gaba da bayanin  cewar ‘ Mun rubuto wannan takarda ne domin mu tunatar da kai shugabatar ma’aikata ta kasa, akan matakin da aka dauka lokacin da ak yi taro na NCE tsakanin ranakun 18 zuwa 22 ga watan Yuli 2016, don haka muna bukatar data mika wannan takarda tamu, zuwa wurin majalisar zartarwa ta kasa, domin su duba su sa hannu, su bada umarni na ayi aiki da hakan wato matakan da aka dauka ,  ga dukkan Hukumomi na gwamnati’’.

Ta bayyana matakan da aka dauka a taro na 39 sun hada da cewar dukkan wadanda suka mallaki takardar shedar ilmi wadanda suka samu aiki na gwamnati da cewar a sasu a matakin albashi na GL 08,wannan matakin da aka dauka da cire fifikon, da kuma karatun PGD wanda suma suna son su kai matakin albashi na GL 17. Wannan gyaran zai sa masu satifiket shedar kammala HND zasu iya kaiwa duk inda mai digiri zai kai a al’amarin aikin gwamnati, bayan sun kammala shi karatun PGD.

Wannan kokari na jan hankali da a fara amfani da yarjejeniyar da ka cimmawa a taron NCE na a daina kawo bambanci tsakanin masu HND  da kuma digiri, ta ci gaba da cewar idan ba a dauki shi wannan matakin ba, yana sa ma’aikata , masu satifiket din HND al’mari yana kasha masu jiki da kuma hana su kuzari yin aiki kamar yadda suka saba.

Kungiyar ta ce wani daga cikin abubuwan da aka cimmawa shi ana amfani da shi, amma an bar saurn wasu har yanzu, ba wata magana dangane da hakan.

Kungiyar ta ci gaba da cewar ‘’ Muna fatan za a bada ita takardar sanarwa t amatakin da aka dauka, saboda ya shafi harkar ma’aikata, don haka muna bukatar iya majalisar zartarwa zata za hannu domin a fara aiwatar da sauran abubuwan.

 

Exit mobile version