Abba Ibrahim Wada" />

Ansu Fati Ya Kafa Tarihi A Barcelona

Matashin dan wasa Ansu Fati ya kafa tarihi a kungiyar Barcelona ta Sifaniya bayan ya buga wasan da Barcelona ta sha da kyar a hannun Borussia Dortmund a Talatar farko ta gasar cin kofin zakarun turai na Champions League na kakar wasa ta 2019 zuwa 2020.

Dan wasan mai shekara 16 da kwanaki 351 a duniya, Fati ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya buga wa Barcelona wasa a gasar Zakarun Turai ta Champions League a tarihin kungiyar.

Kafin wannan lokaci dai dan wasa Bojan Krkic ne ke rike da kambun, inda ya buga wasa tsakanin Barcelona da Lyon a shekarar 2007 yana dan shekara 17 da kwana 22 a duniya a wancan lokacin.

Celestine Babayaro na Najeriya shi ne ke rike da kambun baki daya a gasar ta Champions League domin ya fara buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Anderlecht yana dan shekara 16 da watanni biyu a duniya.

Tun bayan fara wasa a gasar LaLiga ta bana, Fati ya ci kwallo biyu tare da taimakawa wajen cin wata daban wanda hakan yasa kociyan kungiyar ya bayyana cewa zai iya maye gurbin Leonel Messi a Barcelona.

An haifi Ansu Fati a ranar 30 ga Oktoban 2002 a kasar Guinea-Bissau da ke yankin Afirka ta Yamma kuma ya zauna tsawon watanni shida a kasar kafin daga bisani ya koma garin Herrera a kudancin Sifaniya bayan mahaifinsa mai suna Bori ya samu aikin tukin mota a fadar magajin garin.

Mahaifinsa ya ce dan wasan ya koma Barcelona ne bayan Albert Puig, daraktan kungiyar ta matasa, ya mika tayin daukarsa sannan kuma Bori ya shaida wa manema labarai cewa bayan daraktan ya kawo masu ziyara har gida, Barcelona ta ba su wurin zama a cikin farfajiyar hedikwatar kungiyar ta matasa saboda haka ne suka koma birnin Barcelona baki daya da zam.

Exit mobile version