Antonio Conte Yana Tattaunawa Da Tottenham

Antonio Conte

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta tuntubi tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Antonio Conte domin nada shi sabon mai horar da ‘yan wasan  kungiyar a sabuwar kakar wasa mai zuwa.

Babu wani tayi da aka yi kawo yanzu, amma an fahimci Tottenham ta tattauna da kocin dan kasar Italiya kuma a yau ake saran wakilan mai koyarwar tare da lauyoyinsa zasu sauka a birnin London domin tattaunawa da shugabannin kungiyar Tottenham.

Antonio Conte ya lashe gasar Serie A da kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan a bana, kofin farko da kungiyar ta dauka tun bayan shekara ta 2010 a watan jiya, daga baya ya bar kungiyar, bayan cimma yarjejeniya da shugaban kungiyar ta Inter Milan, Steben Zhang.

Tottenham ta yi wa tsohon kocinta Mauricio Pochottino tayin ko zai sake karbar aikin jan ragamar kungiyar a makon jiya sai dai kuma Paris St Germain ba ta da shirin rabuwa da dan kasar Argentinan.

Tottenham ba ta da mai koyarwa tun bayan da ta kori Jose Mourinho ranar 19 ga watan Afirilu ta nada na rikon kwarya Ryan Mason, wanda yaja ragamar kungiyar har zuwa wasannin karshe na kakar wasa ta bana.

Tottenham  ta kammala kakar wasan Premier ta kakar nan a mataki na bakwai a teburi, ta kuma samu gurbin buga Europa League na badi inda ta kammala kakar wasan bana a saman kungiyar Arsenal.

Conte ya lashe kofin Premier League a shekarar 2016 zuwa 2017 a kakar farko da ya karbi akin kocin Chelsea, amma ta sallame shi bayan da ya ci FA Cup da yin na biyar a teburi a kaka ta biyu a Stamford Bridge.

Conte mai shekara 51 a duniya ya ja ragamar Inter Milan zuwa gasar Europa League ta kakar wasan 2019 zuwa 2020 da kuma tazarar maki biyu tsakaninsa da Jubentus wadda ta lashe kofin bara.

Amma a bana Inter Milan ta dauki Serie A da tazarar maki 21 tsakaninta da Jubentus ta hudu a teburin babbar gasar Italiya, ya kuma kawo karshen Serie A tara da kungiyar ta Jubentus ta lashe a jere.

Inter Milan ta dauki Serie A na bana kuma na 19 kenan jumulla tun saura wasa hur-hudu a karkare kakar bana da maki 91, ita ce ta biyu a tarihi da ta kammala wasannin da maki da yawa.

 

Exit mobile version