Connect with us

KASASHEN WAJE

Antonio Guterres Ya Yi Kira Da A Hada Kai a Dukkanin Fannoni Don Yaki Da Korona

Published

on

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga kasashen duniya, da su yi hadin gwiwa, da cudanya da juna daga dukkanin fannoni, wajen shawo kan kalubalen lafiya dake addabar sassan duniya, sakamakon yaduwar cutar numfashi ta Korona.

Mr. Guterres wanda ya yi wannan kira, yayin ganawarsa da manema labarai ta kafar bidiyo a shekaran jiya Alhamis, yayin kaddamar da cikakken shirin MDD na yaki da Korona, ya ce ya zama wajibi dukkanin sassan MDD, da na hukumomin yankunan duniya, da cibiyoyin hada-hadar kudade na kasa da kasa su hada karfi da karfe, wajen shawo kan matsalolin da wannan annoba ta haifar.

Jami’in ya ce cudanyar dukkanin sassa na iya zama managarcin ginshikin tsarin gudanarwa a duk inda aka bukaci hakan.

Guterres ya kara da cewa, kalubalen da kasashen duniya ke fuskanta na da yawa, kama daga cutar Korona, da sauyin yanayi, zuwa batun nuna wariyar launin fata da rashin daidaito tsakanin al’umma.

Daga nan sai ya jaddada bukatar dake akwai ga shugabannin duniya, da su yi hangen nesa, tare da rungumar salon hadgin kai, duba da muhimmancin sa ga rayuwar daukacin bil Adama, musamman a wannan gaba da duniya ke cikin wani mawuyacin yanayi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: