Anya Akwai Kungiyar Da Za Ta Iya Taka Wa Real Madrid Birki A Gasar Zakarun Turai?

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tana neman lashe kofin zakarun turai sau uku a jere kuma na 13 a tarihi a wannan shekarar bayan da kungiyar takai wasan kusa dana karshe bayan ta doke kungiyar Jubentus a wasan da suka fafata a baya.
Duk da cewa nasarar da Real Madrid tasamu akan kungiyar kwallon kafa ta Jubentus tana cike da kalubale da cece kuce bayan da masu kallon kwallon kafa na duniya musamman masu adawa da kungiyar suka bayyana cewa alkalin wasan dayayi alkalancin wasan Real Madrid da Jubentus ya nuna son zuciya ta hanyar bawa Real Madrid bugun fanareti.
Real Madrid dai tana neman lashe wannan gasar karo na uku a jere sai dai abune mai wahala duba da irin kungiyoyin da suka rage a gasar kawo yanzu da suka hada da Bayern Munchen da Roma da kuma kungiyar Liberpool ta kasar ingila.
A ranar Juma’a ne hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai taraba jadawalin yadda ragowar kungiyoyin hudun da suka rage zasu fafata inda aka hada Real Madrid da Bayern Munchen sai kuma Roma wadda tayi waje da Barcelona zata fafata da kungiyar Liberpool wadda itama tayi waje da Manchester City a gasar.
Sai dai ko yaya wasannin za su kasance?

Bayern Munchen Da Real Madrid
Kungiyoyin Real Madrid da Bayern Munchen sun hadu sau 24 a tarihi a gasar zakarun turai inda Real Madrid ta lashe wasanni 11 itama Bayern Munchen ta samu damar lashe wasanni 11 sannan aka buga canjaras sau biyu.
Sai dai a haduwar da akayi Real Madrid ta zura kwallaye 37 yayinda itama Bayern Munchen ta zura kwallaye 36 a duka wasannin da kungiyoyin suka buga a tarihi.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tafi kowacce kungiya yawan lashe gasar bayan data lashe sau 12 a tarihi sannan kuma kungiyar ta lashe guda uku cikin shekaru hudu sai kuma Bayern Munchen wadda take neman lashe kofin karo na shida a tarihi rabon da kungiyar ta lashe gasar tun shekarar 2013 lokacin da kungiyar ta doke kungiyar Borussia Dortmund ta kasar Jamus.
A cikin haduwar da kungiyoyin sukayi sau 24 a tarihi kungiyar kungiyoyin biyu sun hadu sau shida a wasan kusa dana karshe inda Bayern Munchen ta samu nasara a haduwa 4 Real Madrid tasamu nasara a haduwa 2 sai kuma a wasan kusa dana kusa dana karshe inda suka hadu sau biyu kuma Real Madrid ce duk tasamu nasara a haduwar tasu.
Kungiyoyin sun kuma hadu sau biyu a zageye na biyu wato wasan falan daya inda Real Madrid ta samu nasara sau daya itama Bayern Munchen tasamu nasara sau daya sai kuma haduwarsu acikin rukuni-rukuni na gasar inda Real Madrid tasha kashi a wasa farko daci 4-2 sai kuma wasa na biyu Bayern Munchen din tasake samun nasara daci 4-1.
Kusan za mu iya cewa duka kungiyoyin sunyi kokari idan muka duba yanayin haduwarsu da kuma yadda kowacce kungiya ta zura kwallaye a ragar yan uwarta, sai dai sun taba haduwa a wasan sada zumunta inda Real Madrid tasamu nasara daci 1-0 ta hannun dan wasa Danilo wanda yanzu yake buga wasa a Manchester City.
Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen dai bata fara gasar wannan kakar cikin nasara ba inda sai da takai har ta kori mai koyar da yan wasan kungiyar, Carlos Ancelotti, dan kasar Italiya amma daga baya kuma kungiyar ta farfado inda har takoma ta daya akan teburin gasar Bundes Liga kuma tuni kungiyar har ta lashe kofin na wannan shekarar.
Sai dai Real Madrid ma abin haka yake itama bata fara buga gasar ta laliga da kafar dama ba kuma kawo yanzu kungiyar tana mataki na uku akan teburin gasar bayan da Barcelona take kan gaba da maki 16 tsakaninta da Real Madrid
Mai koyar da ’yan wasan kungiyar Real Madrid, Zinedine Zidane yana fuskantar kalubale a wannan kakar na lashe kowanne irin kofi sakamakon gasar zakarun turai ce kawai gasar data rage masa bayan da Barcelona tayi musu nisa sannan kuma anyi waje da kungiyar a gasar cin kofin Copa Del Rey.
Hakan ya sa Zidane ya ke cikin matsin lamba daga bangaren magoya baya da kuma shugabannin kungiyar na ganin ya lashe gasar cin kofin zakarun turai domin ya tsira da aikinsa.
Real Madrid dai zatayi iya kokarinta don ganin ta samu nasara a gasar domin lashewa amma kuma abune mai wahala ganin yadda ita kungiyar ta Bayern Munchen zata lashi takobin ramuwar cin da Real Madrid din tayi mata a shekarar data gabata.
Dan wasa Cristiano Ronaldo dai shine yafi kowanne dan wasa zura kwallo a raga a gasar ta wannan shekarar sannan kuma kawo yanzu ya buga wasanni 11 a jere yana zura kwallo a raga.
Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen dai ta buga wasanni 20 a wasanni daban daban batare da an samu nasara akanta ba a gida sannan kuma kungiyar tana yawan zura kwallo a raga musamman idan tana buga wasa a gida.
Za a buga wasan farko ne a filin wasa na Allianz Arena dake birnin Munich a ranar 27 ga watan nan na Aprilu sannan kuma wasana biyu zaizo ranar 3 ga watan Mayun wata mai kamawa.

Liberpool Da AS Roma
A karo na farko dan wasa Muhammad Salah zai koma birnin Rome domin fuskantar tsohuwar kungiyarsa ta Roma wadda ya bari watanni takwas da suka gabata zuwa Liberpool akan kudi fam miliyan 36.
Kungiyar kwallon kafa ta Roma ce abin kallo a wannan haduwar da akayi bayan data doke kungiyar Barcelona a wasan kusa dana kusa dana karshe da suka fafata a kwanakin baya wasan da yaja hankalin yan kallo a duniya.
A wasan farko da suka buga Roma ce tayi rashin nasara daci 4-1 yayinda wasa na biyu kuma Roma tasamu nasara daci 3-0 wasan da yabawa yan kallo mamaki ganin yadda Roma tayiwa Barcelona dukan tsiya.
Ita ma kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ta doke Manchester City ne daci 3-0 da kuma 2-1 gida da waje kenan duk da cewa Manchester City ce take kan gaba a gasar firimiya kuma kusan za’a iya cewa ta lashe gasar ta wannan kakar.
A shekarar 1984 kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ta doke Roma a wasan karshe na gasar ta zakarun turai a wasan da aka fafata a filin wasan na Roma inda Liberpool ta lashe wasan 4-2 bayan bugun fanareti, tun da farko dai wasan 1-1 aka buga.
Gaba daya kungiyoyin sun hadu sau biyar inda Liberpool tasamu nasara a wasanni biyu Roma tasamu nasarar wasa daya sannan aka buga canjaras a wasanni biyu.
Masana dai suna ganin cewa kungiyar kwallon kafa ta Liberpool cezata samu nasara a wasanni biyun da zasu fafata sai dai kuma idan aka kalli yadda Roma tayi waje da Barcelona a gasar za’a iya cewa itama kanta Roma zata iya bawa Liberpool matsala.
Itama dai kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ana ganin zata samu nasara akan Bayern Munchen a haduwar da zasuyi biyo bayan a yan shekarun nan kungiyar Real Madrid tana yawan samun nasara akan kungiyar Bayern Munchen.
Real Madrid ta lashe gasar zakarun turai guda uku cikin shekaru hudu wanda hakan yake nufin kungiyar ta mamaye kwallon kafar nahiyar turai a yan shekarun nan kuma wannanne karo na uku a jere kenan idan har kungiyar ta sake lashewa.
Shin akwai kungiyar da zata iya takawa Real Madrid birki a cikin kungiyoyin da suka rage a gasar?

Exit mobile version