Abba Ibrahim Wada" />

Anya Mbappe Zai Iya Maye Gurbin Messi A Duniya?

Sa’ilin da Messi da Mbappe suka rungume juna bayan karawa tsakanin Faransa da Argentina, sai ya zamanto kamar wata alama ce ta komawar kwarewar Messi kan Mbappe.
Daukacin wadanda suka kalli wasan da aka yi tsakanin Faransa da Argentina na cin kofin duniya a Rasha, sun bar filin wasan tare da yakinin cewa sun kalli wani wasa na musamman, wanda za a dade ana tunawa sannan kuma daya daga cikin ‘yan wasan da suka buga wasa a filin da ya burge kowa
Shekarun Kylian Mbappe 19 ne kacal, amma ya samu nasarar zura kwallo biyu a wannan karawa, ya kuma yi wasa mai kayatarwa inda har ya samo wa kasarsa bugun fanareti wanda shi ne ya haifar da kwallo ta farko da aka zura a ragar Argentina, a karawar wadda aka tashi Faransa na da kwallo 4, Argentina na da 3.
Wannan wasa ya fito da kwazon Faransa, kuma ya nuna cewa za ta iya taka muhimmiyar rawa, kila ma ta samu nasarar lashe kofin na duniya a karo na biyu a tarihinta.
Mbappe bai zo duniya ba a lokacin da kasarsa Faransa ta lashe kofin duniya, sa’ilin da ta karbi bakuncin gasar a shekarar 1998.
An haifi dan wasan ne a ranar 20 ga watan Disamba na shekarar 1998, kuma yanzu haka yana wasa ne a kungiyar Paris St-Germain da ke Faransa, a matsayin aro daga Monaco.
Amma ana sa ran PSG din za ta saye shi kan kudi Fan miliyan 165.7 idan an kammala gasar cin kofin duniya kuma tuni tattaunawa tayi nisa tsakanin Monaco da PSG akan dan wasan.
Hakan zai sa ya zama dan wasa na biyu mafi tsada a duniya, kasa da yadda PSG din ta sayi dan wasan Brazil Neymar, daga Barcelona a kan kudi Fan miliyan 200
Mbappe na da hazaka sosai ciki har da tunani cikin hanzari, yana amfani da dukkanin kafafunsa yadda ya kamata, ya iya cin kwallo da ka, yana da kwazo, sannan ya iya hangen inda zai zura kwallo a cikin raga.
Bayan karawar tsakanin Faransa da Argentina, ga abin da tsohon dan wasan Ingila Alan Shearer ya ce game da Mbappe: “A shekara 19, a ce ya yi wasa mai kayatarwa irin wannan a gaban Lionel Messi, yayin da miliyoyin al’umma ke kallo, wannan ba karamar hazaka ba ce.”
Mbappe dai Shi ne matashin dan wasa mafi karancin shekaru da ya ci kwallo biyu a wasa guda daya a gasar kofin duniya tun bayan Gwarzon dan wasan Brazil Pele, da ya ci biyu a wasan karshe tsakanin Brazil da Sweden a shekarar 1958.
Haka kuma a wani labarin, Kylian Mbappe, ya bayyana cewa duk alawus din da za’a dinga bashi a gasar cin kofin duniya bazaiyi amfani dasu ba kuma zai bayar dasu domin tallafawa nakasassu domin a cewarsa ba sai an biyashi ba zai yi wa kasarsa aiki.
Dan wasan dai yana karbar alawus din fan dubu goma sha bkawai a duk wasa a gasar cin kofin duniya kuma kudin zai karu idan har kasar Faransa tafito daga cikin rukuni a gasar kuma tuni sun fito har sun kai matakin wasan kusa dana kusa dana karshe.
“Zan sadaukar da abinda ake bani ga wata hukuma wadda take kula da nakasassu domin taimakawa saboda a matsayina na dan kasa nagari ba dole sai an biyani ba zan wakilci kasa ta” in ji Mbappe
Wannan mataki da dan wasan yadauka yasa wasu daga cikin ‘yan wasan tawagar Faransa suma sun dauki aniyar irin wanann taimako sai dai har yanzu ba’a bayyana sunayen yan wasan ba amma kamar yaddara hoto ya bayyana akwai dan wasa Nebil Fekir da Paul Pogba da kuma Ngolo Kante.
A yanzu dai Mbappe ya zura kwallo uku a gasar cin kofin duniya bayan da tun farko ya zura kwallo daya a wasan Faransa da kasar Peru acikin rukuni.
Kungiyar kwallon kafa ta PSG dai za ta biya fam miliyan 166 domin siyan dan wasan bayan daya koma kungiyar a matsayin aro a kakar wasan data gabata daga kungiyar kwallon kafa ta Monaco ta kasar Faransa.

Exit mobile version