Connect with us

LABARAI

APC A Bauchi Ta Tsaida Buhari Da M.A A Matsayin ‘Yan Takararta A Zaben 2019

Published

on

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC (NEC) reshen jihar Bauchi sun amince da tsaida shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar a matsayin ‘yan takararsu a zaben 2019 da ke tafe.

Hakan na zuwa ne biyo bayan wani taron da masu ruwa da tsakin suka gudanar a dakin taro na gidan gwamnati da ke jihar Bauchi a ranar Alhamis, zaman wanda ya gudana a karkashin jagorancin shugaban APC na Bauchi, Alhajin Uba Ahmad Nana, inda masu ruwan suka tafka muhawara kan kudurin daga bisani suka samu yarjewa kan matsayar.

Wakilinmu ya shaida mana cewar an yi muhawarar ce bayan da Alhaji Adamu Bello dan majalisar da ke wakiltar mazabar Giade a majalisar dokokin jihar Bauchi ya gabatar da kudurin neman a tsaida Buhari da Muhammad Abubakar a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa da gwamnan jihar Bauchi a zaben 2019.

Kudurin wanda ya samu mara bayan Rifkatu Samson Danna, Inda suka bayyana cewar wannan shine matakin da ya dace su dauka domin ci gaban kasa da jihar a Bauchi.

Da yake jawabi shugaban jam’iyyar APC na jihar Bauchi, Alhaji Uba Ahmad Nana ya shaida cewar sun yi hakan ne domin masu ruwa da tsaki su tattauna kan ababen da suka jibinci babban zaben da ke tafe, yana mai shaida cewar zaman nasu ya kuma jaddada matsayar da NEC reshen jihar suka dauka na yin amfani da wakilai Delegates a wajen fitar da gwanaye na jam’iyyar.

Da yake jawabinsa a wajen taron masu ruwa da tsakin gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi ya jawo hankalin masu alhalin fitar da gwanaye na jam’iyyar da suka kasance masu adalci wajen aikinsu domin fitar da nagartattun jagororin domin amfanar  talakawa.

Gwamnaan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Abdu Sule Katagum ya shaida cewar Buhari ya yi kokari wajen kyautata Nijeriya musamman kan yaki da Boko Haram, farfado da tattalin arziki da sauransu.

Ya ce, “An amince mun kuma yarda da tsaida shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar APC a zaben da ke gaba. Sannan, mun amince mun kuma yarda da tsaida gwamnan jihar Bauchi, Muhammadu Abdullahi Abubakar a matsayi dan takararmu na gwamna a zaben 2019 da ke tafe,” Inji Katagum

Gwamnan yana mai shaida cewar shugaban kasa ya yi kokari wajen kyautata Nijeriya, don haka suna nan domin su mara masa baya don ya kai ga ida aiyukan da ya faro. Daga bisani kuma ya gode wa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a bisa wannan amincewar da suka yi na tsaida Buhari da gwamnan Bauchi a matsayin ‘yan takarar APC a zaben 2019.

“Buhari ya yi kokari sosai wajen kyautata rayuwar ‘yan Nijeriya ga kuma yaki da boko haram da dakile cin hanci da rashawa a Nijeriya,” Inji shi

Ya kuma karyata zancen nuna wariya a tsakinin ‘yan takarar jam’iyyar, “Duk wanda ya zo ya ce shi ne gwamna ya saya masa fom ko shi ne dan takarar gwamna ya fitar, wallahi karya yake yi. gwamna ya shafa fada shi kowa ya fito ya nemi mutanensa kuma kowani dan APC nasa ne, don haka masu cewa shi ya tsaida su karya suke yi masa,” Inji Katagum

Baya ga hakan, gwamnan ya kuma gargadi delegate kan amsar na goro don fitar da gwani, “Tun da za a yi amfani da delegate wajen fitar da gwani ne, don haka ina kira a yi aiki da tsoron Allah a ji tsoron Allah a zabi wanda suka dace, domin idan aka ce kowani dan takara sai ya zaga kan delegate ya yi musu abun da zai yi musu karshe za a zabi jagororin da basu cancanta ba,” A cewar shi

Da yake karin haske wa ‘yan jarida kan wannan matsayar da suka dauka, shugaban jam’iyyar APC na jihar Bauchi, Uba Ahmad Nana ya shaida cewar sun amince da tsaida Buhari da Muhammad Abubakar a matsayin ‘yan takarar ne domin muhimman aiyukan da suka shimfida wa wadanda suke jagoranta.

Ya na bayyana cewar sun tattauna hadi da fitar da matsayi a matsayinsu na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, “Yau mun gana domin reshen jam’iyyar APC na jihar Bauchi ta tabbatar da goyon bayan shugaban kasa da kuma tsaida shi a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarmu a zaben 2019 da ke tafe,”

Bayan haka, ya bayyana cewar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun kuma amince hadi da tsaida matsaya kan sun tsaida gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar a matsayin dan takararsu na gwamna a zaben 2019 da ke tafe.

Uba Nana yana mai shaida cewar za su tabbatar da yi wa kowani dan jam’iyyar adalci a kowani lokaci, ya kara da cewa sun baiwa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar zarafin tattaunawa daga karshe suka tsaida matsaya kan Buhari da M.A su tsaya musu a babban zaben 2019.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: