APC Ba Ta Da Dan Takarar Da Ya Wuce Buhari A 2019 —Sarkin Yaki

Daga Shu’aibu Yusuf, Abuja

An bayyana cewa matukar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana aniyar sake yin takara a zaben 2019 mai zuwa, to jam’iyyar APC da sauran al’ummar kasar nan ba su da wani ban takarar da ya wuce shi.

Wani dan kasuwa da ke kasuwar Wuse, Abuja Alhaji Abdullahi Abubakar, wanda aka fi sani da Sarkin Yakin Muhammadu Buhari ne ya bayyana haka a zantawarsa da wakilinmu a Abuja cikin  makon da ya gabata.

Sarkin Yakin ya ci gaba da bayyana cewa idan aka yi la’lari da irin abubuwan da Shugaba Buhari ya yi a hawansa mulki, musamman a harkar tsaro da yaki da rashawa da sauran muhimman fannoni, to kuskure ne babba a ce ’yan Nijeriya suna da wani dan takara ba shi ba.

Alhaji Abdullahi ya kara da cewa ya zuwa yanzu kusan duk albawuran da shugaba Buhari ya yi lokacin yakin neman zabe ya cika su. Ya ce, Buhari ya yi alkawarin zai kawo karshen Boko Haram, yau kuma Boko Haram ta zama tarihi. Haka kuma batun yaki da cin hanci da rashawa, kowa na ganin yadda ake fafatawa a wannan fanni.

Da yake tsokaci game da asusun bai-baya da gwamnatin Buharin da fito da shi kuwa, Alhaji Abdullahi yabawa ya yi da wannan tsari, wanda ya ce tsarin ne ya kawo karshen matsalar tattalin arzikin da aka fuskanta a kasar nan. “Don haka ne nake kira ga al’ummar kasar nan su goya wa Shugaba Buhari baya don ganin ya cimma duk manufofinsa da ya sa a gaba don ci gaban kasar nan,” in ji shi.

 

Exit mobile version