Daga Khalid Idris Doya
Tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, na musamman kan harkokin hulɗa da jama’a Doyin Okupe a ranar Alhamis ɗin da ta gabata a garin Ibadan ya misalta jam’iyya mai mulki ta APC da kuma jam’iyyar PDP a matsayin jam’iyyun da suka gama amfani a fagen siyasa a wannan lokacin gabaki ɗaya.
Okupe wanda ke jawabi a wurin taron shekarar 2017 na masu ruwa da tsaki na kudu maso yamma na jam’iyyar ‘Acccord’ a garin na Ibadan ya bayyana jam’iyyu biyun a matsayin jam’iyyun da zamaninsu da kuma amfaninsu ya ƙare, inda ya bayyana cewa tuƙinsu da jan ragamarsu ya daina aiki a wannan lokacin.
Ya ce; “PDP da APC manyan motoci ne masu shekaru sosai waɗanda suke tsufansu ya shafi tushen yadda suke gudanarwa. A yau PDP da APC dukkaninsu sun tashi a aiki sun gama aikinsu. PDP tamkar motace wacce ta lalace ta dawo tana ribas da baya-baya, ita kuma APC tamkar ƙarfe ne da ya karye don haka dukkaninsu sun lalace babu aikin da za su iya yi”. A cewarsa
Da yake jawabin godiya ga membobin jam’iyyar a bisa amincewa da suka yi da wannan sabuwar jam’iyyar, Ajaja ya bayyana cewa jam’iyyar tana da ƙarfi sosai a kudu maso yamma, a bisa haka ne jam’iyyar za ta taka rawa sosai wajen fatattakar APC da PDP domin tasu ta ƙare a fagen siyasar ƙasar nan.