Connect with us

RIGAR 'YANCI

APC: Mu Na Goyon Bayan kungiyar Gwamnonin APC – Arc. Kangiwa 

Published

on

A jiya ne shugaban jam’iyyar APC a jihar Kebbi, Arc. Bala Sani Kangiwa ya bayyana cewar” a matakin jam’iyyar APC a jihar Kebbi muna goyon bayan dukkan Matakin da kungiyar Gwamnonin ci gaban jam’iyyar APC ta kasa a karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu wato ( APC progress Gobernor’s forum) kan tabbatar da cewa rikicin jam’iyyar na cin gida a kan shugabanci da kuma wasu matsalolin na ganin cewa sun dunke duk wata baraka da ke akwai a cikin jam’iyyar, inji shugaban jam’iyyar APC a jihar Kebbi”. Saboda hakan muna tare dasu dari bisa dari.

Shugaban jam’iyyar ya bayyana hakan ne yayin da ya kira taron manema labaru a jiya a Birnin-Kebbi don bayyana matsayar jam’iyyar APC a jihar ta Kebbi kan irin namijin kokarin da kungiyar Gwamnonin APC ta keyi wurin ganin cewar jam’iyyar APC bata rushe ba a karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi.

Bisa ga hakan ya ke kira “ga sauran Shuwagabannin jam’iyyar APC na jahohin kasa nan da kuma mambobinsu dasu baiwa kungiyar Gwamnonin APC a karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi goyon baya don kara samun nasarar dakile dukkan matsalolin da ke damuwar jam’iyyar APC tun daga Matakin kasa har zuwa jahohin da kuma kananan hukumomin domin a kasance tsintsiya madaurin ki daya a cikin jam’iyyar ta APC a duk fadin kasar Najeriya baki daya”.

Ya ci gaba da cewar ” dakatar da shugaban jam’iyyarsu na kasa, Adams Oshiomhole ya biyo bayan dakatar dashi da mazabarsa a jihar ta Edo tayi masa wanda Babbar kotun daukaka kara ta gwamnatin Tarayya ta tabbatar da hakan, inda ta ce ” dakatarwar da aka yiwa shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole bisa ka’idar doka ya ke”. Bisa ga hakan ne ta tabbatar da sauke shi daga shugabancin jam’iyyar ta APC.

Saboda haka ya zama wajibi ga uwar jam’iyya ta bi umurnin kotu domin jam’iyyar APC mai bin umurnin dokokin ce, inji shi”.

Har ilayau shugaban Jam’iyyar na APC a jihar ta Kebbi Bala Sani Kangiwa ya ce ” muna godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan irin kokarin da yayi na daukar hukunci da kuma tabbatar da cewa jam’iyyar APC ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali batare da wata matsala ba”. Hakazalika da kuma bada umurnin gaggawa ga duk ‘ya’yan jam’iyyar ta APC dasu janye dukkan kararakin da suka shigar a gaban kotutukan kasar nan da ya shafi jam’iyyar.

Haka kuma ya kara da cewar ” muna taya sababbin Shuwagabannin kwamitin NWC na uwar jam’iyyar APC a matakin kasa da aka bawai wa jagorancin rikon kwarya don tabbatar da cewa a cikin watanni shidda sun gudanar da zaben maye gurbin Mambobin NWC na kasa da aka zabi Gwamnan jihar Yobe a matsayin shugaban Kwamitin rikon kwarya na NWC na watanni shidda, wanda yin hakan ya kawo karshen matsalar NWC na jam’iyyar da ake fama dashi, inji Bala Sani Kangiwa”.

Daga nan ya godewa dukkan ‘ya’yan jam’iyyar APC na kasa kan irin goyon bayan da su ke bayar wa don ci gaban mai amfani ga mulki APC ga ‘yan kasar Najeriya baki daya. Haka kuma daga karshe yayi kira ga Shuwagabannin da kuma mambobin jam’iyyar APC mu ci gaba da hakuri da junna da kuma yiwa Shuwagabannin jam’iyyar da’a domin daurewa dimokradiyya a kasarmu Nijeriya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: