Connect with us

MANYAN LABARAI

APC Ta Cire Sunan Ministoci Biyu Daga Tsayawa Takara

Published

on

Jam’iyyar APC ta cire sunayen ministocin Buhari biyu daga tsayawa takarar gwamna a jihohin su, ministocin sun hada da Aisha Alhassan ministar mata, da Adebayo Shittu ministan sadarwa.

Jam’iyyar ta bada dalilin cire sunan Shittu, inda ta bayyana cewa dalilin rashin tantance shi din, shine rashin takardar hidimar kasa ta NYSC da bai samu halarta ba.

Amma basu bayyana dalilin rashin tantance Aisha Alhassan din ba, amma mutane da dama suna ganin hakan yana da alaka da wata magana da aka taba jin ta tana yi, inda take bayyana Atiku tsohon mataimakin shugaban kasa a matsayin uban gidanta.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: