APC Ta Fara Sabunta Rijistar Mambobi A Bauchi

Mambobi

Daga Khalid Idris Doya,

Jam’iyyar APC a jihar Bauchi a ranar Talata ne ta kaddamar da fara aikin rijista ga sabbin mambobi da kuma sabunta wa mambobinta shaidar kasancewa ‘ya’yan jam’iyyar, aikin da zai shafe tsawon mako biyu ana gudanarwa.

Da ya ke jawabi yayin kaddamar da fara aikin a unguwar Nufawa da ke cikin kwayar jihar, shugaban kwamitin gudanar da aikin sabuntawa da rijistan mambobin jam’iyyar da aka tura aiki a jihar Bauchi, Alhaji Abdul’aziz Bello, ya yi bayanin cewa wannan rijistan damace ga kowani dan kasan da shekarunsa suka kai kuma yake da sha’awar shiga cikin jam’iyyar da yayi rijista da jam’iyyar domin samun shaidar kasancewar danta.

Kana, hakan kuma wata damace da zai baiwa mambobin jam’iyyar zarafin sabunta rijistansu domin cigaba da kasancewa a cikin jam’iyyar, “Duk wani da ke sha’awar kasancewa mamban wannan jam’iyyar, muddin shekarunsa ko nata ya kai 18 to zai iya yin rijistan nan,” a fadinsa.

Ya sha alwashin gudanar da aikin bisa gaskiya da adalci tare da bin dukkanin matakan da uwar jam’iyyar ta gindaya musu domin tabbatar da yin aikin cikin kwanciyar hankali ba tare da tashin hankali ba.

Ya nemi dukkanin magoya da masoyan jam’iyyar da su mutunta dokoki da ka’idojin da aka fito da su, kana su yi kokarin kiyaye ka’idar kariya daga cutar Korona a yayin da suke shiga layin sabuntawa ko rijista don kasancewa cikin halastattun ‘ya’yan jam’iyyar.

Shi ma da yake jawabinsa, mai rikon mukamin shugaban jam’iyyar APC a jihar Bauchi, Alhaji Uba Ahmad Nana, ya jinjina wa uwar jam’iyyarsu ne a bisa kyakyawar tsari da ta samar na baiwa kowani dan Nijeriya zarafi da damar da zai kasance a cikin jam’iyyar.

Nana ya ce ta wannan hanyar sabunta rijista ko yin sabo ne mutum zai zamu damar zabin jagororin jam’iyyar a yayin babban taron da za ta yi da zarar ta kammala aikin rijistan a fadin kasar nan.

Ya kuma nuna cewa, tabbas har yanzu APC tana da kwarin gwiwar kwace mulki daga hannun jam’iyyar PDP a babban zaben 2023 dake tafe, inda ya bukaci magoya bayan APC su cigaba da amsa sunansu na tsintsiya madaurinki daya.

Exit mobile version