Daga Umar Faruk, Birnin-Kebbi
Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi ta gudanar da taron masu Ruwa da tsaki na jihar a jiya, a dakin taro na masaukin shugaban kasa da ke Birnin-kebbi.
Taron dai ya samu halartar manyan masu Ruwa da tsaki na jihar ta kebbi da manyan Ma’aikatan gwamnatin , sun hada da Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, maitamakin kakakin majilasar dokoki ta Jihar, memba Muhammad Buhari Aliero, Ambassada Isah Muhammad Argungu, Shugaban Jam’iyyar APC ta jihar kebbi, Barista Attahiru Maccido, mataimakan shugaban jam’iyyar APC na yankuna uku na jihar da kuma membobin majalisar dokoki ta jihar kebbi.
Sauran sun hada da shugaban jam’iyyar APC na kananan hukumomi 21, Shugabanin kananan hukumomin mulki a jihar, Sakataren Gwamnatin jihar ta kebbi Babale Umar Yauri, Shugaban Ma’aikatan gidan Gwamnatin Suleiman Muhammad Argungu, da kuma Mai bada shawara ga Gwamna kan harakokin Siyasa,Yusufu Haruna.
A jawabin da shugaban jam’iyyar APC na jihar, Barista Attahiru Maccido ya gabatar a wurin taron ya bayyana cewa uwar jam’iyya ta kasa ita ce ta gudanar da wani taro irin wannan da manufar duba kiraye- kirayen da wasu bangarorin nan kasar ke yi, inda ta kafa kwamiti na wasu Gwamnomin da wasu manyan ‘yan jam’iyyar ta APC, domin binciken ra’ayin kowanne yankin kasar nan kan sake gyaran fasalin kasa. Kan wasu tsare-tsare na tafiyar da mulkin kasar nan.
Har ila yau, ya ce saboda hakan ne aka aike wa da kowacce jiha da jam’iyyar APC ke mulki takardar umurnin gudanar da taron masu ruwa da tsaki domin fito da shawarwarin yadda za a shawo kan wannan kiraye-kirayen da ake ta ci gaba da yi, inda za a duba halin gyaran ko rashin yi.