APC Ta Kori Danbilki Kwamanda Da Magoya Bayansa A Kano

Danbilki

Daga Ibrahim Muhammad,

A halin da ake ciki dai jam’iyyar APC a jihar Kano ta dakatar da Alhaji Danbilki Kwamanda daga shugabancin kwamitin dattawan mazabar Zaitawa da ke cikin Karamar Hukumar Birni, tare kuma da korarsa daga jam’iyyar gaba daya.

 

Cikin wata sanarwa daga hannun Kakakin jam’iyyar na Mazabar, Auwal Kaboyi, ya bayyana cewa duk Shugabannin Mazabar Zaitawa da na Karamar Hukumar Birni da na jiha da na shiyya da na yanki, duk sun rattaba hannu a takaradar dakatarwar.

Haka kuma sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa jam’iyyar ta haramta wa duk wani danta hulda da Danbiki a jam’iyyance.

 

Ta ci gaba da bayyana cewa daukar wannan mataki ya zama dole domin ta kauce wa fadawa cikin hadari, musamman a lokacin zabe, musamman bisa la’akari da yadda ya ke tallar dan takara tun jam’iyyar ba ta bayar da daman yin hakan ba.

 

Sanarwar ta kuma bayyana wasu zunuban Kwamandan da cewa yana yi wa jam’iyya zagon kasa, tare da furta wasu kalamai na nuna cin fuska ga Shugaba Buhari da Gwamna Ganduje.

 

Haka kuma wakilinmu ya ci karo da wata takarda ta korar Kwamandan, mai dauke da sa hannun duk shugabanni  jam’iyyar na Mazabar ta Zaitawa.

Exit mobile version